Tashar Internet ta mujallar 'Makomar karni na 21' ta kasar Argentina ta ba da labarin cewa, wani rahoton nazarin da aka bayar a gun taron shekara-shekara na tsarin jijiyoyin da ke bayar da bayanai ga kwakwalwa na kasar Amurka ya bayyana cewa, yin wasa da kayayyakin kida yana iya kara dangantakar da ke tsakanin bangaren hagu da bangaren dama na kwakwalwar yara, ta haka yawan girman corpus callosum za ta karu da kashi 25 cikin dari.
corpus callosum wani bangare ne da ya hada da bangaren hagu da na dama na kwakwalwa tare. A shekara ta 1995, Mr. Gottfried da ya gudanar da binciken ya gano cewa, game da masu kide-kide da suka kaddamar da yin wasa da kayayyakin kida kafin shekarunsu ya kai 7 da haihuwa, corpus callosum nasu sun fi kauri.
Mr. Gottfried da abokan aikinsa Mary Forgeard da Ellen Winner sun gudanar da bincike ga yara 31 kan kwakwalwarsu ta yin amfani da na'urar daukar hoton kwakwalwa wato MRI. Lokacin da shekarun wadannan yara ya kai 6 da haihuwa, sun gudanar da binciken farko gare su, sun kuma gudanar da bincike na biyu gare su yayin da shekarunsu ya kai 9 da haihuwa.
A cikin binciken farko, yara shida sun rinka yin wasa da kayayyakin kida a kalla awoyi 2 da rabi a ko wane mako. Kuma a cikin 'yan shekarun da shekarunsu ya kai 6 zuwa 9 da haihuwa, yawan girman corpus callosum nasu ya karu da kashi 25 cikin dari bisa dukkan yawan girman kwakwalwarsu. Amma game da yaran da su kan yi wasa da kayayyakin kida bai kai awoyi 2 a ko wane mako ba da kuma wadanda suka daina yin wasan, ba a gano girman irin wannan corpus callosum ba. Dukkan yaran da suka tsaya tsayin daka kan yin haka ne da kayayyakin kida na Piano da Violin, wadanda suke bukatar yin amfnai da hanaye biyu tare.
To, yanzu sai ku shakata kadan, daga baya kuma za mu yi muku wani bayani daban game da dangantakar da ke tsakanin sauraron kide-kide da kuma lafiyar jiki.
A kwanan nan, kungiyar kula da ilmin hauhawar jini ta kasar Amurka ta bayar da wani rahoton nazarin cewa, game da mutanen da ke kamuwa da hauhawar jini, sauraron kide-kide har na tsawon rabin awa a ko wace rana zai ba da taimako wajen rage hauhawar jini.
An labarta cewa, manazarta sun gudanar da wani gwaji ga mutane 48 da shekarunsu ya kai 45 zuwa 70 da haihuwa wadanda suke kamuwa da cutar hauhawar jini, inda suka raba wadannan mutane cikin rukunoni biyu, mutane 28 da ke cikin wani rukuni sun saurari kide-kide na gargajiya da na kasar Indiya har mintoci 30 a ko wace rana, sauran mutane kuma sun ci gaba da zaman rayuwarsu na da.
Daga baya kuma manazarta sun gano cewa, sakamakon da aka samu bayan da aka yi gwajin har mako daya da kuma makwanni hudu, mutanen da suka tsaya tsayin daka kan sauraron kide-kide a ko wace rana, bugun jininsu ya samu raguwa a bayyane. Amma sauran mutane ba su samu kyautatuwa ba a fannin bugun jininsu.(Kande Gao)
|