Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-07 13:01:06    
Sashen wasan harbin faifai da sauri na filin wasan harbi na Beijing

cri

Masu karatu, a kafar babban dutse na Cuiweishan a yammacin birnin Beijing, akwai wani filin wasan harbi mai kyan gani. Shi ne filin wasan harbi na Beijing. Tun bayan kafuwarsa a shekarar 1955, kullum kungiyar wasan harbi ta kasar Sin ta mayar da shi a matsayin muhimmin sansanin aikin horaswa. Dimbin 'yan wasa gwanaye sun bullo a kan dandamalin ba da lambar yabo na gasar wasannin Olympic daga wannan filin wasa. A wannan shekara, za a yi shirye-shiryen wasan harbin faifai da sauri a gasar wasannin Olympic ta Beijing a filin wasan harbi na Beijing. 'Yan wasa masu yawa daga wurare daban daban na duniya za su taru a nan, za su yi takara mai tsanani a nan, inda zakarun gasar wasannin Olympic da ba a iya kidaya yawansu ba suka taba samun aikin horaswa.

Sashen wasan harbin faifai da sauri na cikin yammacin filin wasan harbi na Beijing. Fadinsa ya kai misalin murabba'in mita 6170. A lokacin gasar wasannin Olympic ta Beijing, zai karbi 'yan kallo kimanin dubu 5. A matsayinsa na filin wasa da aka yi masa kwaskwarima da kuma fadada shi, an fara sabuntawa da kuma ajiye na'urorin zamani a cikinsa tun daga ran 24 ga watan Maris na shekarar 2006. Kuma an kammala dukkan ayyuka a watan Agusta na shekarar bara. A gaskiya dai, ba a gamu da matsala ba a harkokin kwaskwarima. Amma a farkon lokacin da aka kaddamar da ayyukan, wani lamari ya girgiza masu yin kwaskwarima.

A watan Mayu na shekarar 2006, an gano wata kushewa a karkashin kasa a dab da filin wasan harbi na Beijing da aka yi masa kwaskwarima. An kuma tono kayayyakin tarihi da yawa a cikin wannan kushewa. Nan da nan masu yin aikin kwaskwarima suka mika rahoto ga cibiyar nazarin kayayyakin tarihi ta Beijing. Wannan cibiya ta aika da ma'aikatanta zuwa wannan filin wasa ba tare da bata lokaci ba. Bayan da suka yi bincike, sun yi mamaki saboda gano kushewu na zamanin da manya da kanana fiye da 100 a cikin wannan filin wasa, wadanda fadinsu ya wuce murabba'in mita dubu 20.

Kushewu masu fadi kamar hakan sun haifar da matsala wajen tono kayayyakin tarihi, sa'an nan kuma, sun dakatar da ci gaban ayyukan kwaskwarima. Ko da yake ba su san lokacin maido da ayyukansu ba, amma masu yin aikin kwaskwarimar sun taimaka wa kwararru masu nazarin kayayyakin tarihi cikin himma, a maimakon kawo koke. Saboda suna ganin cewa, kayayyakin tarihi sun fi ayyukansu muhimmanci. Suna iya gaggauta yin ayyukansu, amma in an lalata kayayyakin tarihi, to, ba za a iya yi musu kwaskwarima ba. A karkashin taimakon masu yin kwaskwarima da kuma kokarin kwararru masu nazarin kayayyakin tarihi, aikin tono kayayyakin tarihi ya kawo karshe yadda ya kamata bayan watanni da dama. An kuma fahimci muhimmancin wadannan kayayyakin tarihi da aka tono a karkashin filin wasan harbi na Beijing, wadannan kayayyakin tarihi na da muhimmanci sosai, kuma suna da daraja sosai.