Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-06 15:44:48    
Wasu labaru game da kananan kabilun kasar Sin

cri

---- Wakilinmu ya samu labari daga wajen cibiyar ba da ilmi da yin jarrabawa ta jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta cewa, yawan sabbin daliban da jami'o'in jihar Tibet suka dauka a shekarar 2008 ya kai 10,211, wato yawan daliban da aka dauka ya kai kashi 60 cikin 100 bisa dukkan dalibai masu yin jarrabawa, yawan dalibai 'yan kananan kabilu na jihar Tibet da aka dauka kuma ya kai kashi 72.7 bisa 100.

Wani jami'in cibiyar ba da ilmi da yin jarrabawa ta jihar Tibet ya bayyana cewa, jihar Tibet wata jihar ce inda 'yan kananan kabilu da yawa ke zama, yawancinsu kuma 'yan kabilar Tibet ne, yawan 'yan makaranta musamman ma 'yan makaranta na kananan kabilu wadanda suke neman shiga cikin jami'a ta hanyar yin jarrabawa sai kara karuwa suke a kowace shekara, sabo da haka an samar da dalibai da yawa ga jami'o'i.

An ce, domin kara yawan 'yan makaranta musamman ma 'yan makaranta na kananan kabilu na jihar Tibet wadanda suke neman shiga cikin jami'a ta hanyar yin jarrabawa su tabbatar da burinsu, bisa hakikanin halin da 'yan kananan kabilu masu yin jarrabawa ke ciki, gwamnatin kasar Sin ta ja layuka 2 masu sha banban dangane da yawan makin da aka tsayar wajen daukar dalibai 'yan kabilar Han da na 'yan kananan kabilu.

---- Yaro Zhang Li, dan kabilar Korea da ke unguwar hadin kai na birnin Jian na lardin Jilin na kasar Sin ya daina karatu tun shekaru 2 da suka wuce, kuma hannunsa ya kone tun lokacin da yake jariri, har ma dukkan yatsunsa na hannaye 2 a hade suke, kuma ba ya iya mika hannunsa, kwanan baya ya sake shiga makaranta bisa taimakon da caji-ofis na tsaron iyakar kasa mai sunan hadin kai da ke birnin Jian ya yi masa.

Yawan manoma 'yan kabilar Korea ya kai kashi 70 cikin 100 bisa na dukan mutanen da ke bakin iyakar kasa na lardin Jilin. Babbar rundunar tsaron lardin Jilin wadda take daukar nauyin tsaron iyakar kasa ta kyautata al'amarin da ke faruwa wajen nuna kauna ga jama'a da samun kwanciyar hankali a bakin iyakar kasa, dukkan sojojin rudunar sun ba da kyautar kudi domin kafa "asusun ba da taimako ga 'yan makaranta", ta yadda 'yan makaranta masu fama da talauci na kabilar Korea zu su iya samun damar shiga makaranta cikin dogon lokaci ta hanyar samun taimakon kudi. A halin yanzu, asusun nan ya riga ya samun kudin Sin fiye da Yuan dubu 200, kuma da akwai 'yan makaranta masu fama da talauci na kabilar Korea wadanda suka samun kudin taimako.