Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-06 15:43:37    
Budurwa Wu Yuzhen wadda ta gaji wakokin kabilar Dong ta kasar Sin

cri

Cikin shirinmu na yau za mu karanta muku wani bayani game da wata budurwa 'yar kabilar Dong wadda kowa ya san ta a shiyyar, wadda kuma ta ci zaben zama mai daukaka wajen yawon shakatawa na kabilar Dong ta lardin Guizhou sabo da ta kware wajen rera wakokin kabilar, sunan wannan budurwa shi ne Wu Yuzhen.

Budurwa Wu Yuzhen wadda yanzu take da shekaru 23 da haihuwa wata 'yar kabilar Dong ce gaba da baya, wadda kuma ta fito daga gundumar Liping da ke kudu maso gabashin lardin Guizhou, tana cike da kuzari kuma tana saukin kusantuwar mutane. Ita kyakkyawa ce kuma tana son murmushi. Lokacin da Wu Yuzhen take yarinya, tana zama cikin hali mai sauki amma da farin ciki. Kamar yadda sauran yara abokanta suka yi, ita ma tun lokacin da take yarinya ta fara koyon wakokin kabilar Dong daga wajen malaman koyarwa na kauyenta. Ta ce,

"Bisa koyarwar da malamai masu ba da ilmi wajen rera wakoki suka yi mini ne, na iya rera wakokin kabilar Dong. A wajenmu da akwai malamai da yawa wadanda suke ba da ilmin rera wakoki, kuma ba a bukatar biyan kudi domin gadar al'adun kabilar Dong ba, wato ba kamar yadda malaman koyarwa suka gabatar da lacca cikin makaranta domin samun kudi ba, a garinmu na kabilar Dong, idan wani yana son koyon ilmin rera wakoki, malaman koyarwa za su iya koya masa ba tare da jin tsoron sadakarwar kome ba. Sabo da haka, mun yi aiki da kyau har haka wajen gadar wakokin kabilar Dong."

Yanayin tattalin arziki na gidan budurwa Wu Yuzhen ba shi da kyau sosai, domin samar mata da kudin karatu cikin jami'a, iyayenta sun je lardin Guangdong don yin aikin kwadago. Bisa matsayinta na babbar diya ko babban da na gidanta, dole ne budurwa Wu daga wani gefe tana yin karatu, daga wani gefe daban kuma tana kulawa da kannenta na maza da mata. Da ya ke budurwa Wu tana zama cikin manyan tsaunuka, tana kishin ganin duniya da ke waje da tsaunuka.

A shekarar 2001, Budurwa Wu Yuzhen ta ci zaben zama daya daga cikin sabbin mambobi guda 10 na kungiyar 'yan fasaha ta wakokin kabilar Dong ta gundumar Liping. Domin kara horar da wadannan samari 'yan wasanni, shugabannin kungiyar 'yan fasaha sun tsaida kudurin aike da su zuwa kolejin koyon ilmin yawon shakatawa na gundumar Liping don su ci gaba da yin karatu. Budurwa Wu ta ce,

"A lokacin da nake karatu da yin aiki a gundumar Liping, na samu digirin matsakaitan makaranta masu koyar da fasahar sana'o'i, bayan da na samu wannan digiri, kuma zan iya samun damar yin karatu cikin jami'a. Daga baya kuma na shiga gasar rera wakoki da aka yi cikin lardinmu wato lardin Guizhou, ni da wasu 'yan mata mun rera wakar kabilar Dong, kuma mun samu lambar yabo ta azurfa, lardinmu ya mai da muhimmanci da kulawa sosai gare mu."

Cikin wadannan shekaru da suka wuce, budurwa Wu Yuzhen tana karatu cikin jami'a, sa'an nan kuma tana nuna wasanni, ta taba je kasashen Rasha da Ukraine tare da 'yan kungiyar fasaha domin nuna wasanni, bayan haka kuma ta ci zaben zama mai daukaka wajen yawon shakatawa ta yankin kudu maso gabashin lardin Guizhou.

A gun bikin baje-kolin duniya da aka shirya a watan Maris na shekarar 2007 a birnin Paris game da yawon shakatawa, Budurwa Wu Yuzhen da wata budurwa 'yar kabilar Dong daban mai sunan Yang Li sun rera waka mai sunan "Kukan gyare" da sauran wakokin kabilar a fadar Versailles domin manyan baki da jami'ai 'yan diplomasiyya na kasashe daban-daban. Fasaharsu wajen rera wakokin kabilar Dong ta burgi mutane da yawa na birnin Paris, musamman ma muryar wakokinsu da kyawawan tufafin kabilarsu sun jawo hankulan manema labaru na kasashe daban-daban sosai, jaridar "Le Parisien" wadda a saman shafi na farkonta ta buga cikakken bayani game da wasannin da 'yan mata na lardin Guizhou na kasar Sin suka nuna.