A ran 27 ga wata, wani jami'in hukumar zirga-zirgar sararin samaniya ta Turai wanda yake kulawa da harkokin hadin gwiwa tsakanin hukumar da kasar Sin da Rasha, da shugaban cibiyar zirga-zirgar jiragen sama ta Rasha sun yaba wa dan sama jannati na kasar Sin sabo da ya samu babbar nasara wajen tafiyar a sararin samaniya.
Jami'in hukumar zirga-zirgar sararin samaniya ta Turai ya ce, dan sama jannati na kasar Sin ya taka rawa mai kyau wajen tafiyar da ya yi a sararin samaniya a koro na farko.
Shugaban cibiyar zirga-zirgar jiragen sama ta Rasha ya ce, kasar Sin ta zama kasa ta 3 wato tana bayan Rasha da Amurka wajen kammala aikin tafiya a sararin samaniya da kanta, wannan kuma ya zama nasara ce ga duk 'yan adam. (Umaru)
|