Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-27 19:53:40    
'Dan sama jannati na kumbo mai lambar bakwai samfurin 'Shenzhou' ya yi taki na farko na Sinawa a sararin samaniya

cri

A ran 27 ga wata da yamma, 'dan sama jannati na kasar Sin Mr. Zhai Zhigang ya bar bangaren kumbo da ke tafiya bisa hanyar zagaya duniya, kuma ya yi taki na farko na Sinawa a sararin samaniya, wato cikin nasara ne, an gama aikin fita daga kumbo na karo na farko na 'yan sama jannati na Sinawa.

Da misalin karfe 4 da rabi na ran 27 ga wata da yamma, bayan da aka tabbatar da lafiyar jikin 'yan sama jannati, mai jagora a kasa ya ba da umurnin fita daga kumbo.

Da karfe 4 da minti 39 da yamma, 'yan sama jannati da ke sanya tufafin da ake yi amfani da su a wajen kumbo wato Zhai Zhigang, da Liu Boming sun bude kofar bangaren kumbo da ke tafiya bisa zagaya hanyar duniya, domin fara ayyuka a sararin samaniya na karo na farko.

Sa'an nan kuma, Zhai Zhigang ya bayar da rahoto ga kasa. Ya ce,

'Na riga na fita daga kumbo mai lambar kawai samfurin 'Shenzhou', ina da lafiyar jiki, ina gaisuwa ga jama'ar kasar Sin, da jama'ar duk duniya.'

Da karfe 4 da minti 45 na yamma, Zhai Zhigang ya sanya tufafi mai suna 'Feitian' da kasar Sin ta yi nazari da kuma kira, ya bar bangaren kumbo da ke tafiya bisa zagaya hanyar duniya, ya yi taki na farko na Sinawa a sararin samaniya.

Zhai Zhigang ya shafe minti kusan 20 yana waje da kumbo, ya tattara na'urorin gwaje-gwaje da aka sanya a wajen kumbo, haka kuma ya yi magana da cibiyar kula da zirga-zirgar kumbo ta Beijing.

'Kowa ya lura, ina Beijing, 'dan sama jannati na kumbo mai lambar bakwai samfurin 'Shenzhou' ya riga ya koma bangaren kumbo da ke tafiya bisa hanyar zagaya duniya.'

Da karfe 4 da minti 58 na yamma, cibiyar kula da zirga-zirgar kumbo ta Beijing ta sanar da cewa, 'dan sama jannati na kasar Sin Zhai Zhigang ya gama ayyuka a wajen kumbo, ya koma bangaren kumbo da ke tafiya bisa hanyar zagaya duniya. Wannan ya alamanta cewa, Zhai Zhigang ya samu nasarar fita daga kumbo a sararin samaniya na Sinawa na karo na farko.

Wannan ya zama taki na farko da Sinawa suka yi a sararin samaniya. A cibiyar kula da zirga-zirgar kumbo ta Beijing, jama'a sun yi tafin hannu raf-raf.(Danladi)