Kakakin ayyukan tafiyar da kumbuna da ke dauke da 'yan sama jannati na kasar Sin Mr. Wang Zhaoyao ya bayyana a ran 26 ga wata a birnin Beijing cewa, da karfe 4 da rabi na ranar 27 ga wata da yamma, 'dan sama jannati na kumbo mai lambar bakwai samfurin 'Shenzhou' zai fita daga cikin kumbo, domin yin tafiya a sararin samaniya.
Mr. Wang ya yi wannan bayani ne a gun wani taron manema labaru da aka shirya a ran nan. Ya ce, 'dan sama jannati zai bukaci rahin sa'a don ya bude kofar kumbo, da kuma gama tafiyarsa a sararin samaniya, da kuma rufe kofar kumbon, haka kuma 'dan sama jannati zai shafe mintoci 20 yana gudanar da harkokin bincike a wajen kumbon. Mai yiyuwa ne, za a yi gyara kan lokacin da zai fita daga kumbo bisa ga halin da ake ciki na tufaffinsa da kuma yanayinsa, ban da wannan kuma, za a dauki matakai da dama, domin rage rikici da mai yiyuwa zai fara a yayin da 'dan sama jannati yake harkoki a wajen kumbon.(Danladi)
|