Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-26 19:45:00    
Kasar Sin ta harba kombo mai dauke da mutane mai lambar Shenzhou 7

cri
A ran 25 ga wata da dare, kasar Sin ta harba kombo mai dauke da mutane mai lamba Shenzhou 7 daga cibiyar harba taurarin dan adam ta Qiuquan da ke arewa maso yammacin kasar don tafiyar da aikin zirga zirgar kumbo mai dauke da mutane a karo na 3 a kasar Sin. Wannan kumbo yana dauke da 'yan sama jannati 3 wadanda za su yi aiki a wajen kumbo a karo na farko. To , jama'a masu sauraro, yanzu za mu karanta muku wani bayanin da wakilinmu ya ruwaito mana da wurin harba kumbon.

A ran 25 ga wata da dare misalin karfe na agogon Beijing a filin harba kumbo mai dauke da mutane da ke cibiyar harba taurarin dan adam ta Qiuquan da ke arewa maso yammacin kasar Sin, kuma bisa umurnin kunna wuta da aka bayar, roka mai tsayin mita 60 wadda ta dura wuta mai walkiya wadda kuma take tura kumbo mai dauke da mutane mai lamba Shenzho 7 ta tashi daga kasa zuwa sararin samaniya.

Bayan minti 20 da aka harba kumbon kuma a cibiyar harba taurarin dan adam ta Qiuquan, Mr. Chang Wanquan, babba mai yin jagoranci ga aikin zirga ziragar kumbo mai daukar mutane na kasar Sin ya sanar da cewa, an samu nasara wajen harba kumbo, wato kumbon ya riga ya shiga hanyar da aka tsayar.

Wannan ya zama karo na 3 ke nan da kasar Sin ta fara tafiyar da aikin zirga zirgar kumbo mai dauke da mutane daga shekarar 2003 zuwa yanzu, aikin nan ya samu kulawa daga sassa daban daban na kasar Sin. A ran nan kafin an harba kumbo mai dauke da mutane mai lambar Shenzhou 7, Mr. Hu Jintao, shugaban kasar Sin ya je wajen cibiyar harba taurarin dan adam ta Qiuquan musamman don yin ban kwana da kuma fatan alheri ga 'yan sama jannati. Bayan samun nasarar harbawar kumbon kuma ya yi jawabi a cibiyar domin taya murna ga nasarar da aka samu wajen harba kumbon. Ya ce, "Nasarar da aka samu wajen harba kumbo mai lambar Shenzhou 7 ta alamanta cewa, an riga an samu nasara ta mataki na farko wajen aikin aikin zirga zirgar kumbo mai dauke da mutane a wannan lokaci. Bayan da kumbo mai lambar Shenzhou 7 ya tashi samaniya lami lafiya kuma ya shiga hanyar zagaya duniya yadda ya kamata, Mr. Hu Jintao ya yi fatan ga mutanen da abin ya shafa cewa, kada ku yi sake a gaba halin da ake ciki, ya kamata ku kara yin kokari domin tafiyar da ayyuka daban daban da kyau a nan gaba, ta yadda za ku yako nasara wajen kammala aikin zirga zirgar kumbo mai lambar Shenzhou 7 daga duk fannoni."

Kumbo mai lambar Shenzhou 7 yana hade da bangarori 3 wato bangaren tafiya bisa hanyar zagaya duniya, da bangaren da za a dawo da shi kasa da kuma bangaren ba da karfin ingizawa domin zirga zirgar kumbo, wadanda duk tsawonsu ya kai mita 9.19, nauyinsu kuma ya kai wajen ton 8. Kumbon zai iya tafiya bisa hanyar zagaya duniya yadda ya kamata har na tsawon kwanaki 3, in hali ya yi kuma zai iya tafiya har na kwanaki 5. Mr. Zhang Bonan, babban mai tsara fasali na kumbo mai lambar Shenzhou 7 ya ce, "Shigar da 'yan sama jannati 3 cikin kumbo mai lambar Shenzhou 7 ya kai ma'aunin koli wajen fasaha. An yi gyare-gyare da gwaje-gwaje da yawa domin biyan bukatun da 'yan sama jannati 3 suke yi cikin kumbon." (Umaru)