Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-26 14:54:40    
Zakara da malaminsa

cri

A rana ta farko da aka fara gasannin wasannin Olympics, Pang Wei, dan wasan kasar Sin wanda ke da shekaru 22 da haihuwa, wanda kuma a karo na farko ne ya shiga wasannin Olympics, ya samu lambar zinariya a gun gasar harbe-harben pistole ta maza ta mita 10, wannan kuma ya zama abin da ba a yi tsammani ba. Amma wani abin da ya kara wa jama'a mamaki shi ne, malaminsa, Mr.Wang Yifu, shi ma ya taba zama zakara a gun wannan gasa a wasannin Olympics na Athens yau da shekaru 4 da suka wuce.

Sau biyu ne malam Wang Yifu ya taba zama zakara a gun wasannin Olympics, kuma bayan da ya yi ritaya daga kungiyar 'yan wasan kasar Sin, a shekarar 2005, ya hau kan kujerar babban malamin kungiyar 'yan wasan harbe-harbe na kasar Sin. Da farko dai, Wang Yifu bai saba da wannan sabuwar rawa sosai ba, ya ce, "Lokacin da na shiga wasa a matsayin dan wasa, to, na yi kokari, na nuna iyawata, na kammala gasa, shi ke nan. Amma a matsayin malamin wasa, kana da 'yan wasa da yawa da za ka horar da su da kuma sauran ayyuka daban daban, wani lokaci, ba ka iya yin kome ba. A lokacin gasa kuma, malamin wasa na iya zauna a baya kawai."

Amma duk da haka, wannan dan wasa zakara ya saba da sabuwar rawarsa cikin sauri. Shekara daya kawai da ya hau kan kujerar malamin wasa, sai dan wasa da ya horar, wato Pang Wei, ya burge duniya. A gun gasar cin kofin duniya ta wasan harbe-harben fistole na maza na mita 10 da aka yi a shekarar 2006, Pang Wei ya zama zakara, kuma a wancan shekarar, Pang Wei na da shekaru 20 kawai da haihuwa. Ga shi yau bayan shekaru biyu, Pang Wei ya zama zakara a gun wasannin Olympics.

Wannan ne karo na farko da Pang Wei ya shiga wasannin Olympics, ga shi kuma an yi gasar a nan kasar Sin, amma duk da haka, a cewar Pang Wei, hankalinsa bai tashi ba. Ya ce, "Na shafe shekaru 4 ina share fagen wasannin Olympics, to, ga shi lokacin wasa ya yi, me ya sa a yi fargaba? Gasa ita ce bikin 'yan wasa, sabo da haka, ya kamata in nuna wa jama'a gwaninta."

A gaban wannan dalibi, ya kamata malaminsa, Wang Yifu ya yi alfahari. Ko da yake a cewar wannan babban malami, Pang Wei ya zama zakara ne sabo da wasu kwararrun 'yan wasa ba su nuna gwanintarsu sosai ba, amma maganarsa ta kuma bayyana ainihin ra'ayinsa, ya ce, "Bayan da ya daga bindiga, na kalle shi daga bayansa, a lokacin, na ji ya yi kama da ni sosai."

To, duka duka wannan shi ya kawo karshen shirinmu na yau, tare da fatan kun ji dadin shirin, kuma za mu sake haduwa a filin nan na "wasannin Olympics nawa" a Jumma'a mai zuwa, kuma da haka, ni Lubabatu daga nan Beijing ke cewa, sai mako mai zuwa, idan Allah ya kai mu.(Lubabatu)