Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-26 14:51:55    
Wasu 'yan wasa nakasassu kadai ne suka iso nan birnin Beijing, amma sun wakilci kasashensu

cri

A ranar 6 ga watan Satumba da dare, an shirya wani gagarumin biki na bude wasannin Olympics na nakasassu na Beijing a filin motsa jiki na kasar Sin, 'yan wasa fiye da 4000 daga kasashe da shiyyoyi 147 sun taru a nan birnin Beijing, masu kallo sama da dubu 90 da ke filin motsa jiki suna lale marhabin da tafin mai yawa ga wadannan 'yan wasa masu karfin zuciya da imani, wadancan kungiyoyin wakilai da ke kunshe da mambobi kadan kuma, sun fi samun marabawa.

A gun wannan wasannin Olympics na nakasassu, wasu 'yan wasa nakasassu kadai ne suka iso nan birnin Beijing, amma sun wakilci kasashensu, kuma sun dauki nauyin makomar al'umma. A cikin shirinmu na yau, za mu kawo muku wani bayani dangane da wadannan 'yan wasa da su kadai ne suka fafata a filayen wasannin Olympics na nakasassu.

A matsayinsa na 'dan wasa daya kawai da ke cikin kungiyar wasannin motsa jiki na nakasassu ta kasar Tanzaniya, Nyabalale 'dan 40 ya shiga gasar jefa kwallon darma ta maza. A ganinsa, wasannin Olympics na nakasassu zai canja zaman rayuwarsa, kuma zai zama dandamalinsa wajen tabbatar da burinsa. Ya ce,

"A lokacin da na san zan wakilci kasarmu, don shiga wasannin Olympics na nakasassu na Beijing, na yi farin ciki sosai. Kullum ina kokari kan wannan. Yanzu, na cimma burina. Wasannin Olympics na nakasassu sun canja zaman rayuwata, kuma sun tabbatar da burina."

Billy Ssengendo, shi ma 'dan wasa daya kawai da ke cikin kungiyar wasannin motsa jiki na nakasassu ta kasar Uganda, yana jin farin ciki sosai saboda samun damar shiga wasannin Olympics na nakasassu na Beijing, Billy ya ce,

"Ina kaunar wasannin motsa jiki, kuma ina jin farin ciki kan wannan. Har ma yanzu ina cikin filin wasannin Olympics na nakasassu."

Saboda rashin samun cigaban tattalin arziki, hukumomin motsa jiki na kasar Uganda ba su bayar da kudi ga kungiyar wakilai ta kasar kan shiga wasannin Olympics na nakasassu na Beijing ba, hukumar wasannin Olympics ta nakasassu ta duniya ce ta bayar da duk kudi na shiga wasannin ga kungiyar wakilai ta Uganda. Ko da ya ke Billy bai samu goyon baya kan kudi ko kadan ba daga kasarsa, amma a matsayinsa na 'dan wasa daya kawai na kasar Uganda da ya shiga wasannin Olympics na nakasassu, Billy ya ce,

"Ina son samun wata lambar yabo, wannan burina ne. Na zo wurin ba domin kudi, ko sauran abubuwa ba, sai dai samu wata lambar yabo ga kasarmu."

'Yan wasa masu shiga wasanni suna fuskantar babban kalubale, musamman ma ga wadanda su kadai ne ke shiga wasannin, amma wannan ba zai kawo tasiri ga wadannan 'yan wasa, da masu horar da su wajen samun lambar zinariya ta wasannin Olympics na nakasassu ba. Zakari Amadou, ya fito ne daga kasar Nijer, wannan ne a karo na farko da Amadou ya shiga wasannin Olympics na nakasassu, kuma shi kadai ne ke wakiltar kasarsa a wasannin, saboda haka, ya san yadda zai sauke babban nauyin da ke bisa wuyansa. Idan ya samu sakamako mai kyau a gasar daukan nauyi, to, jama'ar kasar Nijer za su yi alfarma kan wannan.

Mai horar da shi Ramatou Yamboto tana fatan Amadou zai iya samu wata lambar yabo mai daraja ga jama'ar kasar Nijer. Ta ce,

"Duk 'yan wasa da suka zo birnin Beijing don shiga wasannin suna fatan samun lambar zinariya, lallai wannan dalilin da ya sa suka zo wurin, muna fatan za su cimma burinsu. Gaskiya ne Amadou yana da karfi sosai kan wannan."

Saboda dalilai daban daban, kwamitin wasannin Olympics na nakasassu na kasar Nijer ya gamu da matsaloli da dama wajen kafa kungiyar wakilai don shiga wasannin Olympics na nakasassu na Beijing, amma duk kasar Nijer ta yi iyakacin kokari don shiga wasannin, Yamboto, mai horar da 'yan wasa ta gabatar da cewa,

"A 'yan shekarun da suka wuce, mun yi ayyuka da yawa kan shiga wasannin Olympics na nakasassu na Beijing. Amadou ya fi nuna kwarewa sosai, saboda haka, mun zabe shi da ya wakilci kasar Nijer don shiga wasannin. Amma, wannan ba ya nuna cewa, sauran 'yan wasa ba su nuna kwarewa sosai ba."

Kamar daidai yadda wannan mai horar da 'yan wasa ta ce, watakila ana ganin wasu 'yan wasanni su kadai ne ke fafatawa a filayen wasannin Olympics na nakasassu na Beijing, amma a hakika dai, su ba kadai ba ne, 'yan uwansu na kasarsu suna nuna musu goyon baya sosai daga nesa.