Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-25 22:34:59    
Harba kumbo mai lambar bakwai samfurin 'Shenzhou' da ke dauke da 'yan sama jannati zai kara sa kaimi ga samun ci gaba a kasar Sin

cri

A ran 25 ga wata da dare, cikin nasara ne, kasar Sin ta harba kumbo mai lambar bakwai samfurin 'Shenzhou' da ke dauke da 'yan sama jannati uku, wadanda za su yi tafiya da nazari da dama a sararin samaniya a 'yan kwanaki masu zuwa, domin share fage ga aikin kafa tashar bincike a sararin samaniya. Wannan nasarar da kasar Sin ta samu ba ma kawai za ta sa kaimi ga kasar Sin wajen samun ci gaba a fannonin kimiyya da fasahohi ba, har ma za ta karfafa kwarewar kasar Sin wajen yin nazari da kirkire kirkire da kasar Sin take da ikon mallakar ilmi da kanta.

Babban manajan kamfanin kimiyya da fasaha na zirga-zirgar samaniya na kasar Sin Mr. Ma Xingrui ya bayyana cewa,

'Kasar Sin ta fara gudanar da aikin harba kumbuna da ke dauke da 'yan sama jannati ne ba da wuri ba, ba kamar lokacin yakin cacar baka ba, a lokacin, kasar Amurka da tsohuwar tarrayar Soviet sun zuba jari, da jama'a, da kuma kayayyaki masu yawan gaske, domin yin gasa a sararin samaniya. Kasar Sin ba ta yi hakan ba, kasar Sin ta gudanar da aikin harba kumbuna ne bisa matakin da ya dace, kuma bisa hakikanin halin da kasar Sin take ciki.'

Babban mai tsara roka da ke dauke da kumbo mai lambar bakwai wato Mr. Jing Muchun ya gaya mana cewa,

'Sha'anin harba kumbuna yana da amfani sosai ga manyan masana'antu na kasar Sin, ciki har da danyun kayayyaki, da na'urorin wutar lantarki. Haka kuma mun riga mun yi amfani da wadannan kayayyaki a masana'antun jama'a.'

A karshe dai, babban mai tsara kumbo mai lambar bakwai samfurin 'Shenzhou' wato Mr. Zhou Jianping ya gaya mana cewa, kumbo mai lambar bakwai samfurin 'Shenzhou' da ke dauke da 'yan sama jannati ya zama na dukkan jama'ar da ke rubanya kokari a fannin harbar kumbuna, haka kuma ya zama na ko wane Basine, har ma ya zama na dukkan 'yan Adam. Ya ce,

'A ganina, yin nazari kan sararin samaniya, da habaka wuraren zaman rayuwa sun zama babban buri na 'dan Adam, haka kuma sun zama babban nauyin da ke bisa wuyan kasar Sin, wadda ta zama babbar kasa ce mai tasowa. Bayan da muka gama wannan aiki, za mu ci gaba da gudanar da ayyukan harba kumbuna, bisa ga kwarewar kasar Sin, ta yadda 'dan Adam zai iya kara tafiya zuwa nesa, da kara samun sababbin abubuwa da ba mu sansu ba a da.'(Danladi)