A ran 25 ga wata da dare, a cibiyar harba taurarin dan adam ta Qiuquan da ke arewa maso yammacin kasar Sin, an harba kumbo mai daukar 'yan sama jannati 3 domin tafiyar da aikin zirga zirgar kumbo mai dauke da mutane a karo na 3 a kasar Sin.
Muhimmin aikin da za a yi wajen harba wannan kumbo mai lamba Shenzhou 7 shi ne wani dan sama jannati na kasar Sin zai fita daga kumbo zai yi aiki a wajen kumbon a koro na farko, za a samu babban ci gaba da kuma sarrafa fasahar da abin ya shafa wajen yin aiki a waje da kumbo, sa'an nan kuma za a yi zirga-zirgar kumbo da tararon dan adam tare, da yin gwaje-gwajen kimiyya da fasaha domin samun yawan adadi game da tauraron dan adam. Bisa shirin da aka tsayar an ce, kumbo mai lamba Shenzhou 7 zai yi tafiya bisa hanyar zagaya duniya, kuma nisan da ke tsakaninsu ya kai wajen kilomita 343. (Umaru)
|