Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-25 20:54:27    
Mr. Hu Jintao ya yi ban kwana da yin fatan alheri ga 'yan sama jannati da ke cikin kumbo mai lambar Shenzhou 7

cri
A ran 25 ga wata Mr. Hu Jintao, shugaban kasar Sin ya je wajen cibiyar harba kumbo ta Jiuquan ta kasar Sin don yin ban kwana da yin fatan alheri ga 'yan sama jannati da ke cikin kumbo mai lambar Shenzhou 7.

Hu Jintao ya bayyana wa 'yan sama jannati 3 wato Zhai Zhigang da Liu Boming da Jing Haipeng cewa,

"Nan gaba kadan za ku tashi don tafiyar da aikin zirga zirgar kumbo mai daukar mutane a karo na 3 a kasar Sin. A nan da farko bisa sunan kwamitin tsakiya na jam'iyya da majalisar gudanarwa da kwamitin soja na tsakiya, kuma da jama'ar kabilu daban-daban na duk kasar, ina muku ban kwana da fatan samun nasara. Zirga zirgar kumbo mai lamba Zhenzhou 7 a sararin samaniya shi ne karo na farko ke nan daga cikin mataki na 2 wajen zirga zirgar kumbo mai daukar mutane na kasar Sin. Na yi imani cewa, bisa cikakken goyon baya na jama'ar duk kasa, da yin shiri sosai daga fannoni daban- daban, kuma halin nagari da kuke da shi ta hanyar yin horaswa cikin tsanaki, ba shakka za ku iya kammala wannan aiki mai cike da alfahari kuma mai tsarki tare da cikakkiyar nasara. Kasar mahaifarmu da jama'ar kasar suna jiran dawowar ku cikin nasara. (Umaru)