Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-24 14:41:04    
Ban yi da-na-sani a matsayin mai jagorar maguji makaho ba

cri
Austine Poland Oritshe, wani mamban musamman na da ya zo daga kungiyar 'yan wasan Olympic na nakasassu ta kasar Nijeriya, ya shiga gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing da aka gudana a ran 6 zuwa ran 17 ga wata a matsayin mai jagorar maguji Olusegun Francis Rotawo na Nijeriya a cikin shirin gudu na mita dari 1 na aji na T11. A sakamakon taimakon da Poland ya bayar, Olusegun da ya taba zama na 2 a gun gasar wasannin motsa jiki ta Afirka ta shekarar 2007 ya zama na 6 a Beijing.

Poland ya gaya mana cewa, ya yi shekaru 3 ko fiye yana matsayin mai jagorar maguji makaho, ya sha shiga gasannin da aka shirya a Nijeriya, ya kuma shiga gasar wasannin motsa jiki ta Afirka a shekarar 2007. A daidai shekara ta 3 da ya zama mai jagorar maguji makaho, Poland ya zo Beijing ya shiga gasar wasannin Olympic ta nakasassu tare da abokinsa Olusegun, sun yi gudu a kan hanyar gudu a filin wasa na kasar Sin wato Bird's Nest.

Kafin ya zama mai jagorar maguji makaho a cikin gasa, Poland ya yi cinikin kifi, amma donme ya nemi zama mai jagorar maguji makaho a cikin gasa? Poland ya gaya mana cewa, mafarkina shi ne jagoranci duniya. Akwai hanyoyi da dama na jagorantar duniya, ko ta hanyarka a jagoranci duniya, ko kuma kai da kanka ka jagoranci duniya. Na kasance mai jagorar maguji makaho a cikin gasa, saboda na fahimci cewa, zan iya aiki tare da makaho.

A ganin saura, watakila a matsayin mai jagorar maguji makaho a cikin gasa, Poland bai iya samun kudi da yawa ba, amma Poland ya ce, kasancewa mai jagorar maguji makaho tare da samun ladan alawas kamar dan wasan gudu. Idan dan wasan ya samu lambar zinariya, kasarsa ce ta samu wannan kyauta, idan gwamnatin ta bai wa dan wasan kyautar yabo, to, kaina jagorar magujin za a ba ka irin wannan kyauta, wato a kasarmu ke nan Nijeriya.

Aikin horaswa ya kan kawo wa dan wasa wahalhalu da yawa, balle ma tilas ne Poland ya yi aikin horaswa tare da wani maguji makaho. Ko a cikin shekaru 3 da suka wuce, wannan saurayi ya yi la'akari da janye jikinsa? Poland ya ce,wani lokaci duniya na canzawa, abubuwa suna wahala. Yayin da abubuwa suka kasance masu wahala a gare ka, ya kasance wasu za su taimaka maka.

A ganin Poland, in ya yi shirin yin takara tare da wani maguji makaho a cikin gasa, to, da farko dai wannan maguji makaho zai iya gaskata da shi. Saboda makafi ba su iya ganin kome ba, shi ya sa da kyar su gaskata saura. Ban da wannan kuma, yana bukatar bayar da hakuri da kuma soyayya. Poland ya bayyana cewa, yana da rayuwarsa, ba za su iya kasancewa tare ba a ko da yaushe. Duk da kasancewa ni mai jagoroar maguji ne. yana da rayuwarsa. Dan wasan shi ma yana da rayuwarsa. Yana da abokansa wadanda ya zaba, kuma abun kaunarsa. Amma yayin gasar wasanni, dole ne su kasance tare. Ko lokacin gasanni ko lokacin barci, dole ne suna tare. Suna matsayin kamar 'yan wasa.

Poland ya kuma yi mana karin bayani kan fasahohin da tilas ne wani mai jagorar maguji makaho ya mallaka. Ya ce, abu na farko a cikin aikin mai jagorar maguji, dole ne su yi aiki tare, zuciya ta kasance daya, tunaninsu ya zo daya. Haka nan kuma, ya zama wajibi tsawonsu ya zo daidai ko kuma ya yi kusa daidai, idan dai ana bukatar a samu nasara.

A matsayin wani mai jagorar maguji makaho a cikin gasa, Poland bai iya bulla a kan dandamalin ba da lambobin yabo ba. Amma in ya zama wani maguji, ya shiga gasanni, to, mai yiyuwa ne zai iya samun lambobin yabo. Ko wannan saurayi ya yi da-na-sani a matsayin mai jagorar maguji makaho? Poland ya ce, bai yi da na sani don bai sami lambar yabo ba. Saboda idan aka ba dan wasa lambar yabo, kamar shi ne aka ba. Saboda shi ne ya sanya ya ci lambar yabon. Saboda za a rubuta a cikin littafin tarihi na Nijeriya, na Afirka, na wasan Olympic cewar, Austine Poland shi ne mai jagorar maguji.(Tasallah)