Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-22 20:35:38    
Labaru game da kananan kabilun kasar Sin

cri

---- Kwanan baya, jihar Xinjiang ta kasar Sin ta kaddamar da jerin matakai domin kara kwarin gwiwar manoma wajen shuka shinkafa, kuma ta hanyar fadada gonakin noman shinkafa ce, za a tabbatar da jimlar shinkafa da za a samu bisa daidaici da inganci.

Wakilinmu ya samu labari daga gwamnatin jama'a ta jihar Xinjiang ta kabilar Uighur mai ikon tafiyar da harkokin kanta, an ce bisa ka'idar "samun shinkafa bisa daidaici cikin jihar, kuma da rara kadan", a wannan shekarar da muke ciki jihar Xinjiang za ta mai da muhimmanci wajen noman alkama, sa'an nan kuma za ta kara saurin aikin kawo albarka wajen noman hatsi daban-daban.

A wannan shekarar da muke ciki, fadin gonakin alkama da aka shuka a yananin hunturu a jihar Xinjiang zai karu har zai kai kadada dubu 620, wato zai karu da kadada dubu 10 bisa na shekarar da ta wuce, matsakaicin yawan alkama da za a girba zai karu har zuwa kilogram 350 daga kowace kadada, ta yadda za a samu tabbaci ga jimlar alkamar da za a girba a shekara mai zuwa za ta wuce ton miliyan 4. Sa'an nan kuma jihar Xinjiang za ta fadada gonakin shuka masara, bisa shirin da aka tsayar an ce yawan masara da za a shuka a shekara mai zuwa a jihar zai kai kadada dubu 70, jimlar masara da za a samu kuma zai kai ton miliyan 6.26.

---- Kwanan baya, wata mahakar kwal mai lamba ta farko ta gundumar Wuzhumuqin ta yamma da ke jihar Mongoliya ta gida mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin ta samu izanin tafiyar da aikinta daga wajen kwamitin gyare-gyare da kuma bunkasa kasar. Sabo da haka manyan mahakan kwal guda 4 na kan fili na jihar dukkansu sun samu iznin tafiyar da aikinsu daga gwamnatin kasar, bisa shirin da aka tsayar an ce, jimlar kwal da za a fitar za ta kai ton miliyan 31 a kowace shekara.

Daga cikin wadannan mahakan kwai, madaidaicin yawan kwal da za a fitar daga mahakar kwal ta farko ya kai ton miliyan 7 a kowace shekara, yawan kudin da aka ware domin gudanar da aikin wannan mahakar ya kai kudin Sin wato Yuan biliyan daya da miliyan 987. Mahaka ta 2 kuma za ta fitar da kwal mai nauyin ton miliyan 5 a kowace shekara, yawan kudin da aka ware kuma ya kai Yuan biliyan daya da miliyan 939. Yawan kwal da za a fitar daga mahaka ta 3 kuma zai kai ton miliyan 14 a kowace shekara, Yawan kwal da za a fitar daga mahaka ta 4 kuma zai kai ton miliyan 5 a kowace shekara.(Umaru)