Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-22 19:48:33    
Tabbas ne gasannin wasannin Olympic biyu dukkansu masu ban sha'awa ne, a cewar Philip Craven

cri

Bayan kusan makonni 2 da aka rufe gasar wasannin Olympic ta Beijing, aka bude gasar wasannin Oympic ta nakasassu ta shekara ta 2008 a nan birnin Beijing. Kwamitin shirya gasannin Olympic na Beijing da hukumomin gwamnatin kasar Sin da abin ya shafa sun riga sun dauki alkawari cewa, za su shirya wata gasar Olympic ta nakasassu mai kayatarwa kamar yadda suka shirya gasar Olympic ta karo 29. Game da wannan alkawari da aikin share fagen gasar wasannin Olympic ta nakasassu da aka yi da kuma cigaban harkokin nakasassu da kasar Sin ta samu, lokacin da Mr. Philip Craven, wani Bature, kuma shugaban kwamitin wasannin Olympic na nakasassu na kasa da kasa yake ganawa da wakiliyarmu a jajibirin gasar wasannin Olympic ta nakasassu, ya ce, ana daukar matakai domin cika wannan alkawari.

"Shugaban kasar Sin Hu Jintao ya taba bayyanawa a fili cewa, za a shirya gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing mai kayatarwa kamar yadda aka shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing. Ana bukatar matakai domin cika alkawari. A hakika dai, dukkan matakan da muka gani a kowace rana yanzu sun gaya mana cewa, tabbas ne wadannan gasannin wasannin Olympic biyu dukkansu gasannin Olympic ne masu kayatarwa."

An gane cewa, alkawarin shirya gasannin Olympic biyu masu kayatarwa da kwamitin shirya gasannin Olympic da gwamnatin kasar Sin suka dauka ya samu yabo sosai daga wajen shugaba Philip Craven na kwamitin wasannin nakasassu na kasa da kasa. Ya taba bayyana cewa yana amincewa da wannan alkawari har sau da dama a wurare daban daban. Sabo da haka, lokacin da yake ganawa da wakiliyarmu, ya sake jaddada cewa, dukkan abubuwan da ya gani kuma ya ji suna nuna wa duk duniya wata alama mai kyau.

Da farko dai, masu shirya gasar wasannin Olympic ta nakasassu suna mai da hankulansu sosai kan aikin shiryawa. Sakamakon haka, cike da imani ne Mr. Craven ya bayyana cewa, tabbas ne za a samu gasannin wasannin Olympic biyu masu kayatarwa. Ba ma kawai ana mai da hankali sosai wajen horar da masu aikin sa kai da samar da ayyuka marasa shinge na zamani bisa bukatun da mutane nakasassu suke nema ba, kuma ba ma kawai za a yi dukkan gasannin wasannin Olympic na nakasassu a cikin dakuna da filayen motsa jiki, ciki har da filin motsa jiki na "Shekar Tsuntsu" da dakin wasan ninkayya na "Water Cube" da aka taba shirya gasar wasannin Olympic ba, har ma wani karamin al'amarin da matan Craven ta samu ya girgiza hankalin Mr. Craven sosai. Ya gaya wa wakiliyarmu cewa, "Matata ce ta gaya mini wannan al'amari. A cikin kwanaki biyu masu zuwa, za a yi taron membobin zartaswa na kwamitin wasannin Olympic na nakasassu na kasa da kasa a nan Beijing. A sa'i daya kuma, matansu za su sha iska a Babbar Ganuwa da Fadar Sarkuna ta Beijing da dai sauran wuraren yawon shakatawa. Bayanan ba da jagoranci ga yawon shakatawa a Beijing da aka ba su dukkansu suna da kyaun gani sosai kamar aka samar a lokacin gasar wasannin Olympic ta Beijing. Tun daga daren da aka kashe wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing, masu shirya gasar wasannin Olympic ta nakasassu sun soma mayar da birnin Beijing, wato 'wani birnin Olympic' da ya zama 'wani birnin wasannin Olympic na nakasassu'. Ba a taba ganin irin wannan hanyar canzawa ba a da da aka yi a tsakanin wadannan gasannin Olympic biyu."

Mr. Craven ya kuma yaba wa na'urorin da ake samarwa a unguwar 'yan wasa ta gasar wasannin Olympic ta nakasassu cewa, "na'urori ne mafi kyau da aka samar a tarihi" kamar yadda Mr. Jacques Rogge, shugaban kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa ya taba yin amfani da shi. Mr. Craven ya ce, lokacin da yake ziyara a unguwar 'yan wasa kafin kaddamar da gasar wasannin Olympic ta Beijing, ya gano cewa, ko da yake an sanya alamar "keken hannu" guda kawai a cikin wani wurin kwana da ke da dakuna ukku, amma a hakika dai, 'yan wasa da suke amfani da keken hannu za su iya yin amfani da su duka. Bayan gasar wasannin Olympic ta Beijing, nan da nan ne an kara alamun "keken hannu" a cikin dukkan dakunan wanka, cikin nasara ne aka mayar da su da su zama dakunan da 'yan wasa nakasassu za su iya yin amfani da su cikin sauki. Sabo da haka, Mr. Craven ya yi mamaki ya ce, wannan ya almanta cewa, masu shirya gasar suna mai da hankulansu sosai, kuma sun riga sun fahimci tunani na "'yan wasa suna kan gaban kome".

Ko shakka babu, masu shirya gasar sun yi dukkan ayyuka ne domin 'yan wasa, suna fatan 'yan wasa za su iya nuna gwanintarsu masu kayatarwa a gun gasar wasannin Olympic ta nakasassu. Game da wannan, Mr. Craven yana cike da imani. Ya ce, tabbas ne za a shirya wata gasar wasannin Olympic ta nakasassu mai kayatarwa kamar yadda aka shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing. Mr. Craven ya jaddada cewa, gasar wasannin motsa jiki ta Olympic ta nakasassu gasa ce da za a yi takara sosai. 'Yan wasa da aka sanya wa kafar jabu ko suke amfani da kekunan hannu za su yi gudu kamar yadda Usain Bolt na kasar Jamaica yake gudu, amma sun fi yin kokarinsu lokacin da suke gwada. A hakika dai, 'yan wasa nakasassu sun riga sun shaida cewa, su da 'yan wasan da suka halarci gasar wasannin Olympic dukkansu 'yan wasa ne masu martaba. Kamar Natalia Partyka, 'yar wasan Pingpong ta kasar Poland ta yi, Mr. Craven ya ce, "'Yan wasa nakasassu suna bayyana karfinsu ta hanyar halartar gasar wasannin Olympic ta nakasassu. Wannan ba sabon al'amari ba ne a kan tarihi. A cikin shekaru 80 da na shekaru 90 na karnin da ya gabata, akwai 'yan wasa nakasassu biyu da suka taba halartar gasar harbe-harbe a gun gasar wasannin Olympic. Bugu da kari kuma, a farkon karnin da ya gabata, akwai dan wasa mai nakasa ya taba samun lambar zinariya a cikin gasar wasan lankwashe jiki a gun gasar wasannin Olympic."

Haka kuma Mr. Craven yana fatan 'yan wasa na kasar Sin za su iya bayyana gwanintarsu a gun gasar wasanin Olympic ta nakasassu. Game da Mr. Hou Bing, jakadan da ke bayyana wa duk duniya ruhun wasannin Olympic na nakasassu wanda ya taba samun lambobin zinariya ukku a cikin gasar tslle-tsalle a gun gasannin wasannin Olympic na nakasassu ukku, Mr. Craven ya ce, "Ba makin da ya samu ya burge ni ba, har ma matakin shigarsa cikin wasannin motsa jiki, ba ma kawai yake wakiltar 'yan wasa nakasassu ba. A waje daya kuma, ba zan manta da shi da matarsa ba sabo da suna kasancewa tamkar ni da matata. Wato, wani dan wasa yana bukatar goyon baya da wani mutum daban ya nuna masa. Matar Hou Bing tana yi kamar haka, wannan kuma muhimmin dalilin da ya sa Hou Bing ya zama wani nagartaccen dan wasa."

Ko da yake Hou Bing ba zai halarci wannan gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing ba, amma Mr. Craven ya yi imani cewa, kungiyar 'yan wasa ta kasar Sin wadda take da karfi sosai da 'yan wasa na sauran kasashe da yankuna wadanda suka sa niyyar neman samun lambobin yabo za su gabatar da wata gasar wasannin Olympic ta nakasassu mai kayatarwa sosai.

Jama'a masu sauraro, a gun gasar wasannin motsa jiki, ban da 'yan wasa, kada a manta da abokansu, wato 'yan kallo. Yanzu Mr. Craven yana farin ciki sosai sabo da Sinawa suke mai da hankulansu sosai kan wannan gasar wasannin Olympic ta nakasassu. Mr. Craven ya ce, "Muna da imani cewa, za a sayar da dukkan tikitoci miliyan 1 da dubu dari 6 na gasannin wasannin Olympic na nakasassu. Kuma za a cika dukkan dakuna da filayen motsa jiki."

Daga karshe dai, Mr. Craven ya gayyaci masu sauraron gidan rediyon kasar Sin da su mai da hankulansu kan gasar wasannin Olympic ta nakasassu.

"Na taba yin wasan kwallon kwando a kan keken hannu, wannan gasa ce mafi wuya. Abin da nake son gaya wa masu sauraron gidan rediyon kasar Sin shi ne, muddin dai ka kalli gasannin wasannin Olympic na nakasassu da kanka, tabbas ne za ka ji farin ciki sabo da yanzu dukkan abubuwa a shirye suke." (Sanusi Chen)