" Muna rokon bako daga nesa ba kusa ba ka tsaya a nan". Tare da jin wannan waka mai dadin ji ta kasar Sin da ihu da masu kallo suka yi cikin farin ciki da kuma tafi raf-raf da aminai daga kasashe daban-daban suka yi a filin wasan motsa jiki mai siffar " gidan tsuntsu" wato " Bird's nest", aka kammala gagarumar gasar wasannin Olympics ta Beijing. Ba ma kawai wannan gasa mai ban sha'awa ta kasance wani abun tunawa ga kasar Sin da kuma Beijing ba, har ma ta sosa ran mutane daga wurare daban-daban na duniya, wadanda gaba dayansu suka bayyana fatansu a kan cewa kasar Sin za ta yi nasarar samun kyakkyawar makoma kamar yadda ta gudanar da gasar wasannin Olympics ta Beijing.
A ranar 24 ga wata, dimbin masu kallo na kasashen dake yankin mashigin tekun Parisa suka yi farin ciki matuka da kallon bikin rufe gasar wasannin Olympics. Cikin makwanni biyu da suka gabata, gasar wasannin Olympics ta daukar hankulan mutane, wadanda sukan yi hira a kai. Wani dan makaranta mai suna Yasir Wissam daga kasar Oman ya fada wa wakilinmu cewa: " Mukan yi kallon wasannin Olympics a gaban akwatin T.V. a kowace rana. Dazu-dazun nan, na kalli bikin rufe gasar wasannin Olympics ta Beijing, wadda ta kasance mafi kyau a tarihin wasannin Olympics. Ina mai sha'awar kallon gasannin da 'yan wasan kasa Sin suka yi tare da abokan karawarsu na sauran kasashe, musamman ma wasan kwallon kwando; Ina son Yao Ming kwarai da gaske domin shi ba nagartaccen dan wasan kwallon kwando na kasar Sin kawai ba, har ma wani shahararren tauraro wasan kwallo ne na duniya, wanda ya kasance wani abun alfahari ne na masu sha'awar wasan kwallon kwando na Asiya".
Kamar yadda dan makaranta Yasir ya yi, masu kallo da dama na kasashen dake yankin shigin tekun Parisa dukkansu sun buga babban take ga gasar wasannin Olympics ta Beijing. A cewarsu, wannan dai ba wai domin gasar wasannin Olympics ta Beijing ta gwada wa mutane gasanni mafiya kayatarwa ba, har ma domin gasar din ta bayyana kyawawan al'adun gargajiya na kaksar Sin ga jama'ar kasashe daban-daban na duniya. Wani injiniya mai suna Fadi-Al-Karim daga kasar Kuwait ya fada wa wakilinmu cewa: " A zahiri dai, an fi yin nasarar gudanar da gasar wasannin Olympics a wannan gami. Lallai wannan gagarumar gasa ta shere ni tun da aka bude ta. Gasar wasannin Olympics ta Beijing tana da wani babban take wato gasar wasannin Olympics ta zamantakewar al'adu. Mu ma muka ji a cikin zukatanmu cewa, ta wannan gasa ce muka samu karin ilimi a fannin tarihi da kuma al'adu na kasar Sin. Da zahihiyar zuciya ce muke fatan kasar Sin za ta yi nasarar samun kyakkyawar makoma kamar yadda ta gudanar da wannan gagarumar gasa''.
Jama'a masu saurare, ko da yake wadannan aminai ba su samu damar zuwa nan Beijing su da kansu ba, amma ga alama,dukansu suna sha'awar wasannin Olympics, suna goyon bayan Beijing, kuma sun yi alfahari da ganin gudanar da gasar wasannin Olympics ta Beijing cikin nasara. Jakadan kasar Sin a kasar Qatar Mista Yue Xiaoyong ya yi farin ciki da fadin cewa : ' Babu makama , gasar wasannin Olympics ta Beijing ta samu nasara domin ta samu goyon baya daga aminai na kasashe daban-daban na duniya. A Beijing, mun ga irin wannan nasara ; A sauran wuraren duniya ma kamar Doha da kuma dukkan kasashen yankin mashigin tekun Parisa, gwamnatocinsu da jama'arsu sun yi farin ciki matuka da ganin nasarar da kasar Sin ta samu wajen gudanar da gasar wasannin Olympics ta Beijing. Kasar Qatar ta tura wata tawaga da ta fi girma a tarihi a wannan gami don halartar wasannin Olympics na Beijing ; Kazalika, mai jiran gadon sarautar kasar ya kuma halarci bikin bude gasar da kuma kallon gasannin. Mu ma mun gode wa gwamnatin Qatar da jama'arta bisa goyon baya da kuma taimakon da suka bayar yayin da ake share fagen gasar da kuma gudanar da gasar wasannin .''
Aminai 'yan Afrika, ko da yake an rigaya an kwo karshen gasar wasannin Olympics ta Beijing, amma duk da haka, 'yan wasan kasashe daban-daban na duniya za su sake haduwa a birnin London na kasar Burtaniya bayan shekaru hudu wato a shekarar 2012, inda za su ci gaba da rubuta sabon shafi mai kayatarwa na wasannin Olympics. Jakadan Burtaniya a kasar Qatar Mista John Hawkins ya fada wa wakilinmu cewa : ' Lallai gasar wasannin Olympics mai kayatarwa ta kawo babban matsi ga London, amma gwamnatin London ta lashi takobin sanya kokari kamar yadda gwamnatin Beijing ta yi. A nan dai, na taya aminai Sinawa murnar nasarar da suka samu wajen gudanar da wasannin Olympics cikin makwanni biyu da suka gabata". ( Sani Wang )
|