Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-19 16:39:05    
A birnin Huhhot ne za a bude gasar wasan Qigong na duk kasar Sin

cri
A ran 20 ga watan Satumba a birnin Huhhot, za a bude gasar wasan Qigong wato wani irin wasan motsa jiki na jan dogon numfashi a karo na 2 na kasar Sin, da akwai kungiyoyin wakilai da suka zo daga larduna da jihohi masu ikon tafiyar da harkokin kansu da birane da ke karkashin gwamnatin tsakiya kai tsaye 29 za su shiga gasar.

Wannan gasar da za a yi tana daya daga cikin jerin bukukuwan wasan Qigong na "yin wasan motsa jiki na dukkan jama'a da shirya wasannin Olimpic tare", cibiyar kula da wasan Qigong ta babbar hukumar wasan motsa jiki ta kasar Sin, da hukumar wasan motsa jiki ta jihar Mongoliya ta gida mai ikon tafiyar da harkokin kanta, da gwamnatin jama'a ta birnin Huhhot su ne suke shirya wannan gasa tare. Kuma da akwai mutane kusan 500 ciki har da 'yan wasa da malaman koyarwa na wasa da alkalan wasa za su halarci wannan gasa cikin kwanaki 3. 'yan wasan kuma za su halarci gasanni iri 4 na kungiya-kungiya ko na mutum daya-daya. (Umaru)