Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-19 16:34:36    
Tarihin wasannin Olympic na nakasassu

cri

Kwanan nan, akwai masu sauraronmu da suka rubuto mana cewa, suna so a ba su tarihin wasannin Olympic na nakasassu, ciki har da A'isha Hassan da ta zo daga garin Funtua, jihar Katsina, tarayyar Nijeriya, da kuma Mudassir Babangida daga Ikko Nijeriya da dai sauransu. Sabo da haka, masu sauraro, a kasance da mu domin sauraron bayaninmu mai ban sha'awa a kan wasannin Olympic na nakasassu.

Nakasassu sun dade suna wasannin motsa jiki iri daban daban, Tun tuni a shekarar 1888, an kafa kulob na wasanni tsakanin kurame a birnin Berlin na kasar Jamus, kuma a shekarar 1922, an kafa hadaddiyar kungiyar wasannin motsa jiki ta bebayen duniya. Bayan yakin duniya na biyu kuma, an sami babban ci gaba wajen bunkasa wasannin motsa jiki tsakanin nakasassu. A lokacin, wasu sojojin da suka nakasa a fagen yaki na Turai, sun fara wasanni domin samun warkewa, wadanda suka zama asalin wasannin motsa jiki na nakasassu na zamanin yanzu. A shekarar 1948, asibitin Stoke Mandeville na Birtaniya ya shirya gasar wasanni tsakanin nakasassu masu amfani da kekunan kuragu. A lokacin, sojoji nakasassu 16 da ke kan keken kuragu ne kawai sun shiga gasar. Daga baya, a kan gudanar da gasar a kowace shekara. A shekarar 1952, sabo da 'yan wasa na kasar Holland sun shiga gasar, shi ya sa gasar ta zama ta kasa da kasa.

Daga bisani, a shekarar 1960, bayan da aka kammala wasannin Olympic, 'yan wasa nakasassu kimanin 400, wadanda suka zo daga kasashe 23 na Turai da Amurka sun taru a birnin Rome, inda suka gudanar da gasar wasannin Stoke Mandeville a karo na 9, wadda daga baya aka amince da ita a matsayin wasannin nakasassu na duniya a karo na farko. Sa'an nan, a shekarar 1976, kungiyar nakasassu ta duniya ta yanke shawarar hada wasannin Stoke Mandeville da wasannin nakasassu na duniya, kuma an gudanar da gasar wasannin Olympic na nakasassu na farko a birnin Toronto na kasar Canada, kuma 'yan wasa nakasassu 1657 da suka zo daga kasashe 38 sun shiga gasar. A shekarar 1988 kuma, kwamitin wasannin Olympic na duniya ya tsai da kudurin cewa, tilas ne a gudanar da wasannin Olympic na yanayin zafi da kuma wasannin Olympic na nakasassu a birni daya. A shekarar 1989, an kafa kwamitin wasannin Olympic na nakasassu na duniya, wato IPC, wanda ya kasance wata kungiyar duniya ta 'yan wasa nakasassu, wanda kuma ke kulawa da harkokin wasannin Olympic na nakasassu da dai sauran wasannin nakasassu. Sa'an nan, a shekarar 2000, kwamitin wasannin Olympic na duniya da kwamitin wasannin Olympic na nakasassu na duniya sun cimma yarjejeniyar cewa, tilas ne birnin da ya karbi bakuncin wasannin Olympic ya gudanar da wasannin Olympic na nakasassu, wato a filayen wasannin Olympic kuma a cikin wata daya bayan da aka rufe wasannin Olympic.

A ran 6 ga watan nan da dare, an yi kasaitaccen bikin fara wasannin Olympic na nakasassu na Beijing a babban filin wasan kasar Sin da ake kira "shekar tsuntsu". A gun bikin, shugaban kasar Sin, Mr.Hu Jintao ya sanar da soma wasannin Olympic na nakasassi na wannan karo.

'Yan wasa nakasassu sama da 4000 tare da malaman wasa da jami'ai sama da 2500, wadanda suka zo daga kasashe da shiyyoyi fiye da 140 sun shiga wasannin Olympic na nakasassu na Beijing, har ma sun fi yawa a tarihi. Ana gudanar da wasannin Olympic na nakasassu na Beijing ne daga manyan fannoni 20, ciki kuwa har da harba kibiya da guje-guje da tsalle-tsalle da kwallon kafa da kwallon kwando da wasan judo da daga nauyi da tseren kwale-kwale da iyo da dai sauransu. Bisa ka'idojin wasannin Olympic na nakasassu, ana gudanar da wasannin ne bisa nakasar 'yan wasa, ta yadda za a tabbatar da adalcin wasannin da kuma tsaro a gasa, kuma gaba daya ne, za a kaddamar da lambobin zinari 471 a gun gasar wasannin Olympic na nakasassu na Beijing. (Lubabatu)