A gun wasannin Olympics na nakasassu na Beijing, a matsayinsa na 'dan wasa daya kawai da ke cikin kungiyar wasannin motsa jiki na nakasassu ta kasar Tanzaniya, Nyabalale zai shiga gasar jefa kwallon darma ta maza. A ganinsa, wasannin Olympics na nakasassu zai canja zaman rayuwarsa, kuma zai zama dandamalinsa wajen tabbatar da burinsa.
Nyabalale, 'dan 40, an haife shi a wani karamin kauye da ke jihar Kigoma ta kasar Tanzania. Yana son wasannin motsa jiki sosai, kuma rashin sauki da ya samu kan aikace-aikace a sakamakon nakasar kafa, bai hana shi da ya yi wasa tare da sauran yara masu lafiyar jiki ba. Ya gaya wa wakilinmu cewa,
"A lokacin yarantakata na kan yi wasa tare da yara masu lafiyar jiki, mu kan yi wasan kwallon kafa, sauran yara sun yi wasan da kafofi, amma ni kuma na yi wasan da hannaye, lallai mun yi hadin kai kamar yadda ya kamata."
Saboda yana da nakasar jiki, don haka, Nyabalale bai shiga makaranta kamar sauran yara ba, amma a lokacin da yake da shekaru 14 na haihuwa, ya shiga wata makarantar nakasassu da ke birnin Dar Es Salaam, inda Nyabalale, wanda ke kwarewa kan motsa jiki tun daga lokacin yarantakarsa ya kara samun damar shiga wasannin motsa jiki. Ya taba wasan wasannin kwallon kwando da nakasassu ke yi a kan keken guragu, da na dambe, da na daukan nauyi, da dai suaransu. Amma, a karshe dai, ya tabbatar da wasannin jefa kwallon darma, da na jefa faifan karfe da su zama wasannin da zai yi a cikin gasa. Nyabalale ya ce,
"A shekarar 2006, na shiga gasar daukan nauyi a gun wasannin kasashe masu zumunci da Ingila da aka shirya a birnin Melbourne na kasar Australian, a lokacin, maki mafi kyau da na samu shi ne kilos 110, da kyar na ke iya samu sakamako mai kyau da wannan maki. Daga baya kuma, na mayar da wasannin jefa kwallon darma, da na jefa faifan karfe da su zama wasannina. A shekarar da ta wuce, na shiga wasannin motsa jiki na Afrika da aka shirya a kasar Algeria, inda na nuna kwarewa sosai, har ma na samu damar shiga wasannin Olympics na nakasassu na Beijing."
Yanzu, ba a samu cikakkun manyan gine-gine kan motsa jiki a kasar Tanzania, sharudan da 'yan wasa suka samu wajen horo su ma ba su da kyau, ta yadda tilas ne 'yan wasa nakasassu na kasar su rage wahalolinsu a cikin ayyukan samun horo na yau da kullum, da kuma kara yin kokarinsu. Nyabalale ya gaya wa wakilinmu cewa, babu kayayyakin horo na fasaha, da wuraren motsa jiki, da kuma rashin abinci mai gina jiki, su ne muhimman daililan da ke kawo tasiri ga sakamakon da 'yan wasa na kasar Tanzania suka samu.
Saboda haka ne dai, ya zama dole Nyabalale ya kan sayar da kayayyakin fasaha da ya kirkiro da tsoffin kayan sauyi na karafa da kuma gasasshen nama a lokatun hutu domin samun kudin rayuwa da kuma bada garanti ga samun horo. Game da irin wannan mawuyacin halin da ya shiga, Nyabalale ya furta cewa,
"In babu wanda ka iya tallafa maka, to tun farko, wajibi ne ya nuna juriya da fuskantar duk wadannan abubuwa da ke gabanka; Kana ka karfafa zuciyarka da kanka cewa 'Dole ne ka yi kamar haka', labuddah haka za ta cimma ruwa.'"
A karshe dai, an saka wa kokarin da Nyabalale ya yi, ya nuna kwarewa sosai a gun wasannin motsa jiki na Afrika, ta yadda ya samu damar shiga wasannin Olympics na nakasassu na Beijing. Kan wannan kyakkyawar dama da ya samu, Nyabalale ya yi farin ciki sosai. Ya ce,
"A lokacin da na san zan wakilci kasarmu, don shiga wasannin Olympics na nakasassu na Beijing, na yi farin ciki sosai. Kullum ina kokari kan wannan. Yanzu, na cimma burina. Wasannin Olympics na nakasassu ya canja zaman rayuwata, kuma ya tabbatar da burina,"
Yanzu, halin da Nyabalale ke ciki kan jiki, da horo yana kamar yadda ya kamata. Tun daga watan Yuni na shekarar da ta wuce, mai horar da shi Namajojo ya soma ba shi horo a dukkan fannoni, kuma sun samu sakamako mai kyau. Namajojo na da imani sosai kan kwarewar da Nyabalale zai nuna a gun wasannin Olympics na nakasassu, ya ce,
"A hakika dai, mun samu sakamako mai kyau a fannoni daban daban wajen shiga wasannin. Nyabalale ya shirya sosai, zai yi iyakacin kokarinsa don yin takara tare da 'yan wasa daga kasashe daban daban."
Shugaban kungiyar wasannin motsa jiki na nakasassu ta kasar Tanzania Jasson Meela yana ganin cewa, ban da samu lambobin yabo ga kasarsu kuma, shiga wasannin Olympics na nakasassu na da ma'ana sosai ga 'yan wasa nakasassu, ciki har da Nyabalale. Ya ce,
"Wannan wata dama ce mai kyau wajen tabbatar da cewa, nakasassu suna da iyawa kamar mutane masu lafiyar jiki, suna iya yin ayyuka daban daban. Gaskiya ne, ba kawai wasannin Olympics na nakasassu ya kawo fata ga Nyabalale, da iyalinsa, har ma ya karfafa imani da kwarin gwiwa ga nakasassu na kasar Tanzania."
|