Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-18 17:15:17    
Saurayi Zheng Fusheng wanda ke fama da ciwo

cri

Saurayi Zheng Fusheng yana da shekaru 38 da haihuwa a wannan shekara da muke ciki.A lokacin da shekarunsa ya kai 21,wani mugun ciwon kashin baya ya same shi ba zato ba tsammani,yana jin zafin ciwon dukkan gabobin jikinsa,ya iya tsaya kawai,ba ya iya dukawa ba,bai iya tafiya ba sai da sanda.Ana shakkar ciwonsa ciwon sankarau babu maganin da ya warkar da shi a duniya.kafin ya samu ciwo,shi saurayi ne mai koshin lafiya, ga shi yanzu ya kasa yin aiki yadda ya kamata, har ma ya sha wahala a zaman yau da kullum.Mr Zheng Fusheng ya ce lokacin da ya ke kwance a kan gado,ba ya iya yin mu'amala da waje ya rasa abin da zai yi kuma ya ji kadaici sosai.

"Ban taba tsammanin samun wannan mugun ciwo a rayuwata ba."

Kafin ciwon ya same shi kamar yadda sauran samari masu koshin lafiya suke da su sa kyakkyawan fatan alheri ga makomarsu.Yayin da yake hira da wakilin gidan rediyonmu,ya ga yara da manyan dake wasa a filin ciyawa da ke gabansa ya ce " Idan wannan ciwon bai same ni ba ni ma ina zama kamar yadda suke cikin 'yanci.Da na sami aiki,ina so in samu kudi in samu wata budurwa,mu zagaya wurare daban daban na duk kasa.zama mai dadi ne da na ke nema a rayuwata,ga shi yanzu ya zama banza'.

Shi Zheng Fusheng,da daya ne kawai da iyayensu su suka samu a lokacin da suke cikin matsakaicin shekaru.Yayin da ya kamu da ciwo,mamarsa ba ta da aikin yi,ubansa ya yi ritaya.Kudin shiga na iyalinsa kudin Sin RMB yuan darurruwa ne kawai a kowane wata.Iyayensa suna tsammani idan dansa Zheng Fusheng ya girma ya samu aiki ya iya ba da taimako ga iyalinsa,ban taba tsammanin za su ci bashi sabo da ciwon dansu ba Uwarsa Wu Xinhua ta ce "Da dana ya samu mugun ciwo ba zato,mun shiga halin kaka nika yi babu mafita, Mun fara shan wahalar zama." Daga nan nauyin dake bisa wuyan iyayen Zheng Fusheng ya kara yawa.Ba ma kudin zaman yau da kullum suke bukata ba har ma da kudin jinya domin dansu. Da Zheng Fusheng suna aiki tukuru ko wace rana dominsa,bai ji dadi ba.Wata rana bayan da ya saurari shirye shiryen gidan rediyo na wurinsa,wata hikima ta fado masa sai ya rubuta wata wasikar neman taimako zuwa ga gidan rediyon.Bai taba tsammanin za a amsa wasikarsa ba,an watsa shi a shiryen shiryen gidan rediyo,mutane masu dinbim yawa sun nuna damuwarsu kan lafiyar Zheng Fusheng.Ma'aikata guda 16 da ke wata masana'anta ta birnin Xuzhou sun kai shi asibit domin yi masa jinya ta hanyar tausasawa,sun nace ga yin haka a yanayin dari ko a yanayin zafi ba su tsaya ba.

A cikin wannan lokaci wani saurayi da ake kiransa Ding Qiang,ya taka muhimmiyar rawa wajen taimakon Zheng Fusheng.Ding Qiang,shi dan makarantar middle school ne na koyon sana'a ta musamman.Da ya ga Zheng Fusheng,ya dauki nauyin kula da shi tare da iyayensa.har ma ya yi amfani da damar da ya samu a lokacin hutu na yanayin hunturu ya kai shi asibitin dake waje da birnin Xuzhou.A lokacin Ding Qiang ne kawai ya ke kula da zaman rayuwa na Zheng Fusheng.Ding Qiang ya ce a ganin sauran mutane su 'yan'uwana ne.

"Abin da na yi ya girgiza shi.Da na gan shi na kan je wurinsa in yi hira da shi da kuma taimaka masa,na yi aiki gwargwadon iyawata,dukkanmu samari ne."

Bisa taimakon da mutane na da'irori daban daban suka ba shi,cutar Zheng Fusheng ta saukaka sosai,har ya iya yin tafiya sannu sannu,ya fara yin tunani cikin nitsuwa.A cikin wani bayaninsa ya rubuta kalamomi haka:tun daga lokacin da nake neman taimako har zuwa yanzu da nake zama cikin kauna na mutane masu dimbin yawa tamkar na fara jin gumin yanayin bazara bayan da na sha sanyi mai tsananni a yanayin hunturu.Na yi farin ciki sosai da samun taimako daga mutane masu dimbin yawa,hankalina ya kasa kwanciya ya kamata in yi wani abu domin mayar da martani ga kauna da suka nuna mini.

"Yayin da sauran mutane ke nuna maka kauna,ya kamata ka mayar musu da kauna,ta haka kuwa kauna ta game ko ina a zamantakewa."

A ran 20 ga watan Afrila na shekara ta 1997,Mr Zheng Fusheng ya cika shekaru 30 da haihuwaA wannan rana ya kawo shawarar kafa wata kungiyar hadin kan masu sa kai ta birnin Xuzhou.Daga ranar nan aikin ya fara yi wa Mr Zheng Fusheng yawa. A cikin shekaru 10 da suka gabata shi Mr Zheng Fusheng da mutane masu sa kai na kungiyar sun tattara kudin taimako na kudin Sin RMB yuan dubu dari hudu don taimakawa marasa lafiya da nakasassu da dama.Daga cikin mutane sama da dubu da Zheng Fusheng da 'yan kungiyarsa masu sa kai suka taimaka da akwai wata yarinya wadda ta yi sa'a,sunanta Juanzi.Yayin da ta kai shekaru 12 da haihuwa,wata cutar jini d ake kira leukaemia a turance ta same ta,iyalinta ya kashe dukan kudin da ya tanada domin warkar da ita cikin wasu shekarun da suka shude.Da Mr Zheng Fusheng ya sami labarin nan,shi da abokansa masu sa kai sun fara tattara kudade daga bisani sun tattara kudaden da yawansu ya kai sama da kudin Sin dubu dari.wanda ya biya bukatun dasa kabushi a jikinta.