Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-17 16:08:36    
Wani bikin da ke cikin bukukuwa 24 na yanayin sararin samaniya na kasar Sin, wato ranar bikin somawar yanayin zafi

cri

Bukukuwa 24 na yanayin sararin samaniya na kasar Sin suna da tarihin da yawan shekarunsu ya kai dubu biyu ko fiye. Su ne abubuwan tarihi na al'adu da mutanen zamani aru-aru na kasar Sin suka samu bayan da suka dudduba da nazari da kuma takaita abubuwa kan yanayin sararin samaniya cikin 'yanci kuma cikin dogon lokaci. Suna iya bayyana sauye-sauyen yanayin sararin samaniya da ruwan sama da sauran sauye-sauyen da ake samu bisa yanayin sararin samaniya da kuma ba da jagoranci ga ayyukan noma, sun ba da tasiri sosai ga abinci da sutura da zirga-zirga da sauransu na dubban iyalai. A takaice dai, an kasa shekara daya cikin matakan lokaci 24 bisa yanayin sararin samaniyia, a kowane matakin, alamar yanayin sararin samaniya ba ta sauya sosai ba, kuma an dora matakin da wani suna. A kowane wata, ana iya samun bukukuwan yanayin sararin samaniya guda biyu. Alal misali, a watan Afril, a farkon rabin watan, an sami ranar bikin Qingming, amma a karshen rabin watan, an sami bikin Guyu.

Bikin shigowar yanayin zafi wato Xiazhi na shekarar da muke ciki ya zo ne a ranar 21 ga watan Yuni . A wannan rana, rana ta haskaka yankuna masu zafi sosai, wato tana haskaka kan layin taswirar duniya na 23.5 na arewa da ikwata. A rabin duniyar arewa, yanayin zafi na da tsawon lokaci a rana, kuma tsawon lokacinsa yana kara karuwa a rana a wuraren da ke nisa da arewa sosai. Dayake kasar Sin tana da makekiyar kasa, saboda haka tsawon lokacin rana na da banbanci sosai a tsakanin arewacinta da kudancinta. Alal misali, a birnin Haikou na lardin Hainan da ke kudancin kasar Sin, yawan tsawon lokacin rana ya kai sa'o'i 13 ko fiye, amma a birnin Beijing da ke arewacin kasar Sin, yawan tsawon lokacin rana ya kai sa'o'i 15, a birnin Mohe na lardin Helongjiang da ke arewacin kasar Sin sosai ya kai sa'o'i 17 ko fiye. Bayan yanayin zafi, wuraren da rana ya haskaka su kai tsaye suna kaura zuwa kudancin duniya a kai a kai, kuma yawan tsawon lokacin rana ya ragu a kai a kai a rabin duniya ta arewa.

Ban da layin iyakar musamman da ke tsakanin rana da dare, ranar bikin somawar yanayin zafi ita ce inda somawar yanayin zafi. Akwai karin magana na kasar Sin da yake cewa, ba za a sami zafi ba in bikin somawar yanayin zafi bai zo ba, kodayake zuwan ranar bikin shigowar yanayin zafi ya bayyana cewa, yanayin zafi ya soma zuwa a gare mu, amma ba lokacin zafi sosai ne ya zo ba, bayan bikin somawar yanayin zafi, zafi sai kara yawa a kai a kai a cikin wani lokaci, wato bayan kwanaki 20 zuwa 30, yanayin zai kara zafi sosai, a wannan lokaci, a wasu wuraren kasar Sin, ana samun zafin da ya kai matsayin koli da centigrade 40.

Bayan wucewar yanayin zafi ke da wuya, a yawancin wuraren kasar Sin, hasken rana ya yi yawan gaske, kuma tsire-tsiren gonaki suna kama sosai kuma suna kara tsawo cikin sauri, sa'anan kuma suna bukatar abubuwa da yawa. A wannan lokaci, ruwan sama zai ba da tasiri ga samun amfanin gona. Ana cewa, ruwan sama da ake yi a ranar bikin shigowar yanayin zafi na da daraja sosai ga aikin noma , amma a wani lokaci, an gamu da bala'i da yawa, kuma ana kan gamuwa da bala'in kwari, saboda haka, ana kan cewa, ana shuka shuke-shuke ba tare da bata lokaci ba, wato a shuka shuke-shuke a daidai lokacin da ba zai wuce tsakar rana ba. Wadansu aka riga aka shuka su ya kamata a kula da su sosai. Kuma ya kamata a cire ciyayi da yawa a gonaki, ana cewa, in ba a cire ciyayi a gonaki a yanayin zafi ba, to abin da aka yi tamkar yadda aka kiwo maciji mai guba da zai cije ka.

Mutanen kasar Sin sun mai da hankali ga kiwon lafiya bisa sharudan yanayin sararin samaniya. In yanayin zafi ya zo, ya kamata ana kasancewa cikin halin sakin jiki tare da farin ciki sosai, kuma ana nuna sha'awa sosai ga halittu dubu dubbai ta yadda halinka yake kasancewa cikin nishadi.

Ilmin likitancin gargajiyar kasar Sin yana ganin cewa, a yanayin zafi, ana gumi da yawa, shi ya sa gishiri ya ragu a jiki, saboda haka zuciya ta kan samu cikas, ya kamata a ci abinci bisa daidaici, a kara cin abinci mai tsami da mai gishiri, amma bai kamata a kara cin abinci mai sanyi tare da mai da yawa ba . (Halima)