Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-17 16:03:36    
Lafiyar jikin iyaye maza za ta ba da taimako kan girman yaransu

cri

Bisa labarin da jaridar Daily Telegraph ta kasar Birtaniya ta bayar a ran 2 ga wata, an ce, kwararrun kasar Denmark a fannin ilmin likitanci sun gano cewa, idan iyaye mata da shekarunsu ya yi yawa lokacin da suke haihuwa, hakan ya kan yi illa ga lafiyar jariransu, to, game da iyaye maza da shekarunsu ya yi yawa da haihuwa kuwa, hakan zai kara yiyuwar mutuwar jariransu sakamakon cututtuka.

Kuma an labarta cewa, kwararru na cibiyar nazari kan cututtuka masu yaduwa ta kasar Denmark sun gudanar da bincike ga jarirai dubu 100 da aka haife su daga shekara ta 1980 zuwa shekara ta 1996, kuma yara 830 daga cikinsu mun mutu kafin su yi girma, kuma yawancinsu su kan mutu lokacin da shekarunsu bai kai daya da haihuwa ba.

Ban da wannan kuma binciken ya gano cewa, game da jariran da shekarun iyayensu maza ya kai fiye da 45 da haihuwa, yiyuwar mutuwarsu ta ninka kusan sau daya idan an kwatanta da jariran da shekarun iyayensu maza ya kai 25 zuwa 30 da haihuwa. Bugu da kari kuma, game da wadannan yara, yiyuwar kamuwa da cututtukan kadaici da farfadiya da kuma cutar da ta shafe tunani ta karu in an kwatanta da sauran yara.

Manazarta suna ganin cewa, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da ingancin maniyyi ya kan samu raguwa tare da karuwar shekaru da haihuwa.

Kowa ya sani, mata su kan kamu da cutar bakin ciki bayan da suka yi haihuwa, amma a kwanan nan, manazarta na kasar Amurka sun nuna cewa, bayan haihuwar yara, iyaye maza su ma suna da yiyuwar kamuwa da cutar bakin ciki. Bugu da kari kuma, idan iyaye maza sun kamu da cutar, to wannan zai yi illa ga kwarewar yaransu wajen magana.

Bisa labarin da mujallar sabbin masu ilmin kimiyya ta kasar Amurka ta bayar, an ce, manazarta na kwalejin likitanci na gabashin jihar Virginia ta kasar Amurka sun gudanar da bincike ga gidaje 5000, daga baya kuma sun gano cewa, lokacin da shekarun yaransu ya kai watanni 9, iyaye mata da yawansu ya kai kashi 14 cikin dari sun kamu da cutar bakin ciki bayan haihuwa yayin da iyaye maza da yawansu ya kai kashi 10 cikin dari suka kamu da cutar.

Manazarta sun nuna cewa, lokacin da shekarun yaran da aka gudanar da binciken gare su ya kai 2 da haihuwa, an yi musu gwaji da kalmomi 50 da su kan yi amfani da su, daga baya kuma an gano cewa, game da yaran da iyayensu maza suka kamu da cutar bakin ciki, matsakacin yawan kalmomin da suke iya ya ragu da 1.5 in an kwatanta da yaran da iyayensu maza ba su kamu da cutar ba. Haka kuma tare da karuwar shekarunsu da haihuwa, gibin da ke tsakanin wadannan yara wajen kwarewar magana zai kara karuwa.

Manazarta sun bayyana cewa, lokacin da iyaye maza suke kamuwa da cutar bakin ciki, lokacinsu na karata littattafai don yaransu zai ragu, amma iyaye mata ba za su yi kamar haka ba.