Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-16 22:01:02    
Kungiyar jiyya ta kasar Rasha ta gudanar da ayyukan ceto a yankunan da ke fama da girigizar kasa na lardin Sichuan

cri

Assalam alaikum, jama'a masu sauraro. Barkanku da war haka, barkanmu da sake saduwa da ku a wannan fili na "kimiyya da ilmi da kuma kiwon lafiya na kasar Sin". Ni ce Kande ke gabatar muku da wannan shiri. Kungiyar jiyya ta kasar Rasha da ke kunshe da masu jiyya 67 kuniya ce ta farko ta duniya da ta isa yankunan da ke fama da girgizar kasa na lardin Suchuan na kasar Sin domin gudanar da ayyukan jiyya. Bayan da suka isa birnin Pengzhou da ke fama da girgizar kasa mai tsanani, sai nan da nan suka gina asibitin bakin daga don ba da agaji cikin gaggawa, da kuma fara gudanar da ayyukan jiyya. To a cikin shirinmu na yau, bari mu leka kungiyar jiyya ta kasar Rasha tare.

Kammala aikin gina asibitin bakin daga don ba da agaji cikin gaggawa ke da wuya, kungiyar jiyya ta kasar Rasha ta samu mutane da suka jikkata na kashin farko. Yang Yixu da shekarunta ya kai 80 da wani abu da haihuwa tana daya daga cikinsu. Lokacin da aka samu girgizar kasa a ran 12 ga watan jiya, ta fadi, kashin bayanta ya karye, kuma ta samu girgizar kwakwalwa kadan. Sabo da girgizar kasa ta lalata asibitocin wurin sosai, inda ba a iya samun kyawawan sharudan jiyya ba, shi ya sa mutane masu ceto suka kai Madam Yang Yixu asibitin bakin daga na kasar Rasha don samun jiyya cikin gaggawa.

Masu jiyya na kasar Rasha sun yi wa Madam Yang tiyata a cikin awa guda da ta isa asibitin bakin daga. Aleksander Ivanus, babban mai ba da umurni na kungiyar jiyya ta kasar Rasha ta gaya wa wakilinmu cewa, dalilin da ya sa kungiyar take iya gudanar da ayyukan ceto kamar yadda ya kamata ba tare da bata lokaci ba shi ne sabo da suna da kayayyakin zamani na tafi-da-gidanka wajen gina asibitin bakin daga. Kuma ya kara da cewa, "Dukkan kayayyakin asibitin suna da saukin hadawa da kwancewa, kuma ba su da nauyi sosai. Ba kawai ana iya jigilarsu da motoci ba, har ma ana iya samunsu ta hanyar jefa su daga jiragen sama masu saukar ungulu da masu dauke da kayayyaki. Sabo da haka, a kan yi kira asibitin 'asibitin tafi-da-gidanka a sararin sama'. Asibitin yana iya samar da ayyukan ba da hidima iri 16 ciki har da aikin ba da agaji da na jiyya da kuma na injiniya."

Kuma Mr. Ivanus ya bayyana cewa, wannan asibitin bakin daga yana iya samar da ayyukan jiyya ga mutane 200 da suka ji raunuka masu tsanani a ko wace rana, kuma ana iya yin tiyata ga mutane 5 zuwa 10 a sa'i daya.

Ban da ceton masu jikkata, masu jiyya na kasar Rasha su ma sun gudanar da ayyukan kwatantar da hankalin mutane masu fama da girgizar kasa. A cikin asibitin bakin daga, wakilinmu ya ga likita Olia Makarova tana gudanar da aikin kwatantar da hankali don wani yarinya da shekarunta ya kai 3 da haihuwa. Bisa labarin da muka samu, an ce, iyayen yarinyar sun ji raunuka masu tsanani a cikin girgizar kasar, kuma ta ji tsoro kwarai da gaske. Madam Makarova ta gaya wa wakilinmu cewa, "Bayan aukuwar girgizar kasa, mutane su kan ji tsoro sosai sabo da mutuwar 'yan iyali da kuma tsoron sake rushewar dakunan kwana da kuma tsaron sake aukuwar girgizar kasa da dai sauransu. Abin da muke yi shi ne yin hira tare da su domin su iya kwantar da zukatansu. Game da yara, muna iya yin zane-zane tare da su domin su bayyana tsoronsu da kuma kyakkyawan burinsu."

Lokacin da muke kusan kammala zantawa da Madam Makarova, wannan yarinya ta yi murmushi a karshe wanda ba safai a kan gan irinta cikin wani lokaci ba. Madam Makarova ta bayyana cewa, tana fatan dukkan mutanen da suka jikkata a cikin wannan girgizar kasa za su sake yin murmushi a lokacin nan gaba na ba da jimawa ba.(Kande Gao)