Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-16 14:42:28    
Sakamakon da aka samu a gun wasannin Olympic na Beijing na nakasassu na ran 15 ga wata

cri

Ya zuwa ran 15 ga wata, ana da kwanaki 3 kawai cikin gasar wasannin Olympic ta Beijing ta nakasassu. 'Yan wasannin kasar Sin sun samu lambobin zinariya 17 a wannan rana, daga nan ne, jimlar lambobin zinariya da kasar Sin ta samu ta kai 80, wannan ya wuce lambobin zinariya 63 da aka samu a gun wasannin Olympic na Athens kuma yana kan gaba a duniya bisa lambobin zinariya.

A ran 15 ga wata, an gama dukkan gasannin iyo na wannan wasannin Olympic na nakasassu. Ana cigaba da kafa sabbin tarihi wajen gasanni a dakin iyo na 'water cube', yawan matsayin bajinta da aka karya ya kai 87, kuma an samu zakaran lambobin zinariya da zakaran lambobi, wato shahararren 'dan wasa Natalie Du Toit na kasar Afrika ta kudu da Matthew Cowdrey na Australia dukkansu sun samu lambobin zinariya 5, haka kuma, Daniel Dias na Brazil ya samu lambobin yabo 9.

A bangaren gasannin guje-guje da tsalle-tsalle, 'yan wasannin kasar Sin sun cigaba da samun lambobin zinariya 6, rukunin 'yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na kasar Sin ya riga ya samu lambobin zinariya 33.

A ran 16 ga wata, ana kusan gama gasar wasannin Olympic ta nakasassu, za a samu lambobin zinariya 37 a wannan rana. Daga cikinsu, gasannin da suka fi jawo hankalin mutane su ne ire-iren gasannin guje-guje.

Za a samu zakaru 4 na wasan kwallon tennis na wheelchair na mata da na maza. Ban da wannan kuma, za a samu lambobin zinariya 2 na karshe wajen gasar daga nauyi ta maza ta ajin kilo 100 da kuma ajin kilo fiye da 100.

Za a samu zakara tsakanin rukunonin Ukraine da Rasha wajen gasar kwallon kafa ta mutane 7 a ran 16 ga wata da yamma. Haka kuma, gasa mafi daraja da aka gano a gun wannan wasannin Olympic na nakasassu ita ce gasar kwallon kwando ta maza ta wheelchair ta karshe tsakanin rukunonin Canada da Australia.(Lami)