Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-15 21:04:42    
Bayanin da wani masanin ilmin kabilar Tibet ya bayar kan ayyukan daidaita da kuma kiyaye al'adun gargajiya na kabilar

cri

Wakar da kuka saurara dazu wata wakar gargajiya ce mai sunan "Tarihin sarkin Gesar" wadda tsoho dan fasaha mai sunan Samdrup wanda ya ba shekaru 86 baya na jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin ya rera, wannan waka wata wakar tarihi ce wadda take da amfani wajen binciken zaman al'ummar kabilar Tibet na tsohon zamani. Cikin shekaru kusan 1,000 da suka wuce, 'yan fasahar gargajiya sun yi ta rera wannan waka daga jikoki zuwa jikoki, sabo da haka suka ci gado kuma suka kyautata abubuwan da aka rera cikin wakar. To, jama'a masu sauraro cikin shirinmu na yau za mu roki Mr. Tsering Phuntsok, mataimakin lshugaban ofishin binciken al'amuran kabilu na cibiyar binciken zaman al'umma ta jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta da ya ba ku labari game da ayyukan daidaita da kuma kiyaye al'adun gargajiya da aka yi a kabilar Tibet.

Tsoho Samdrup wanda ya ba shekaru 86 baya wato ya fi yawan shekaru da haihuwa daga cikin 'yan fasaha na kabilar Tibet wajen rera wakar gargajiya mai sunan "Tarihin sarkin Gesar", kuma yana daya daga cikin 'yan fasaha mafi kyau wajen rera wakar. Sabo da a zamanin da jihar Tibet ta ci baya sosai wajen aikin ba da ilmi, shi ya sa tsoho Samdrup bai taba shiga makaranta ba. Mr. Tsering Phuntsok, mataimakin shugaban ofishin binciken al'amuran kabilu na cibiyar binciken zaman al'umma ta jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ya bayyana cewa, "Lokacin da ake kidayar mutane cikin karnin da ya wuce, an gano wannan dan fasaha wato Samdrup. Bisa abubuwan da ya fada ya ce, a lokacin da yake da shekaru 11 da haihuwa, wata rana ya yi wani mafarki lokacin da yake barci a filin ciyayi, bayan da ya farka daga barci sai ya iya rera wakar "Tarihin sarkin Gesar".

A jihar Tibet, mutane da yawa sun yi daidai kamar tsoho Samdrup wato sun yi barci kuma sun yi mafarki, amma bayan da suka tashi daga barci sun iya rera wakar "Tarihin sarkin Gesar". Halin musamman na su shi ne, dukkansu ba su iya karatu da rubuto ba ko kadan, amma suna da basira kwarai. Mr. Tsering Phuntsok, mataimakin shugaban ofishin binciken al'amuran kabilu na cibiyar binciken zaman al'umma ta jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ya bayyana cewa, "Yawancin 'yan fasaha masu rera wakoki sun fito ne daga iyalan manoma da makiyaya masu fama da talauci, kafin samun 'yancin kasar Sin, wasunsu suna tafiyar da zama ne ta hanyar rera wakoki, suna yawon gantali ko'ina, zaman rayuwarsu ba a zo a gani ba ne. Suna yawo da dabbobi a makiyaya kuma suna rera wakoki, daidai kamar yadda 'yan fasaha na kasar Greece suka rera wakar tarihi mai sunan "Homerros" a zamanin da."

Mr. Tsering Phuntsok ya ci gaba da cewa, tun bayan da aka fara ayyukan jaddada dimokuradiyya daga shekarar 1959 a jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta zuwa yanzu, al'adun zamani na jihar suna ta samun bunkasuwa a kowace rana, sa'an nan kuma an ba da kariya da kuma bunkasa al'adun gargajiya na jama'a.

Mr. Tsering Phuntsok ya kuma bayyana cewa, cikin shekaru 50 da suka wuce, jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta yi ayyuka da yawa da ba a taba ganin irin su ba a tarihi wajen bincike da daidaita da kuma buga litattafan adabi da fasaha na gargajiya na kabilu. Ya ce, "A zamanin da, addini ya kai muhimmin matsayi a jihar Tibet, ba a mai da hankali kan wakokin gargajiya wadanda suka samu karbuwa daga wajen jama'a ba, har zuwa lokacin samun 'yancin jihar, da yin ayyukan jaddada dimokuradiyya, musamman ma bayan da aka fara yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, gwamnatin kasar Sin ta mai da muhimmanci sosai wajen kiyaye da kuma bunkasa al'adun jihar Tibet, ya zuwa yanzu an riga an ziyarci 'yan fasaha masu rera wakokin gargajiya 57, kuma an yi musu rakodin wakokin da yawan su ya kai 103, ban da wannan kuma an rubuta wakokin da suka rera fiye da 90, daga cikin su kuma har da 73 wadanda aka riga aka daidaita da kuma buga kundayensu."