Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-15 20:40:50    
Wasu labaru game da kananan kabilun kasar Sin

cri

---- Bisa labarin da karamar kungiyar shugabantar aikin yaki da talauci da ake yi a jihar Mongoliya ta gida mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin ta bayar kwanan baya an ce, zuwa karshen shekarar 2007, yawan mutane masu fama da matukar talauci na jihar Mongoliya ta gida ya rugu daga miliyan daya da dubu 160 na shekarar 2000 zuwa mutane dubu 400.

Tun bayan da aka fara gudanar da "Tsarin yaki da talauci a kauyukan kasar Sin daga shekarar 2001 zuwa ta 2010" zuwa yanzu, an riga an kauratar da mutane fiye da dubu 50 cikin lokuta 5, sabo da haka an daidaita matsalar zaman rayuwa da samun bunkasuwa ga wasu mutane masu fama da talauci, kuma an yi tallafi ga mutane dubu 350 wajen sana'a da fasaha, daga cikin su da akwai mutane fiye da kashi 80 bisa 100 wadanda za su juya hankulansu wajen sana'o'in masana'antu da yin hidima ga jama'a cikin birane da garuruwa.

Sa'an nan kuma, an kara mai da hankali wajen yin muhimman gine-gine a wurare masu fama da talauci, kuma an kyautata sharudan aikin gona da na kiwon dabbobi sosai. Ban da wannan kuma, sharudan ba da ilmi ga yaran da ke wadannan wurare sun samu kyautatuwa sosai, kusan an ce dukkan yaran da suka isa shiga makaranta ana shigar da su, kuma an sassauta halin karancin likitoci da magunguna da ake ciki a wadannan wurare.

---- Kwanan baya, hadaddiyar kungiyar musulmi ta kasar Sin ta buga kuma ta fara sayar da babban littafin zane-zane mai sunan "Sabon halin da musulmin kasar Sin ke ciki" a nan birnin Beijing.

Wannan babban littafin zane-zane mai sunan "Sabon halin da musulmin kasar Sin ke ciki" ta bayyana manyan sauye-sauyen da musulmi 'yan kabilu daban-daban suka samu wajen zaman al'umma da zaman yau da kullum, da zaman addini da al'adu da ba da ilmi da yin mu'amalar da kasashen waje da kuma fannin bunkasa tattalin arziki cikin shekaru 30 da suka wuce wato tun bayan da aka fara yin gyare-gyare da bude kofar kasar Sin ga kasashen zuwa yanzu.

Wani jami'in da abin ya shafa na hadaddiyar kungiyar musulmi ta kasar Sin ya bayyana cewa, makasudin sayar da wannan littafin zane-zane shi ne domin kara fahintar da aminai musulmi da sauran mutane na kasashe daban-daban kan kasar Sin da musulmin kasar na yanzu.