Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-15 17:37:06    
Birnin Beijing ya yi kokarin daukar matakan samar wa nakasassu guraban aikin yi

cri

Bisa dokokin kasar Sin, dole ne hukumomin gwamnati da kungiyoyin jama'a da kamfanoni da masana'antu sun samar da wasu guraban aikin yi ga nakasassu. Amma sabo da wasu kamfanoni da masana'antu ba su iya samar da guraban aikin yi da suke dacewa da nakasassu ba, dole ne sun biya wasu kudade ga gwamnati domin taimakawa nakasassu ta hanya daban.

Jama'a masu sauraro, a nan kasar Sin, ba ma kawai wasu nakasassu sun nemi guraban aikin yi da kansu ba, har ma gwamnati ko wasu mutane sun kafa wasu masana'antun jin kai domin daidaita matsalar samar wa nakasassu guraban aikin yi. Masana'antar samar da na'urorin lantarki ga jirgin kasa na shiyyar Fengtai ta birnin Beijing na daya daga cikin irin wadannan masana'antun jin kai. Shugaban wannan masana'anta Qi Fubin ya bayyana cewa, yanzu a cikin dukkan 'yan kwadago 120, akwai 'yan kwadago nakasassu 55. Mr. Qi ya ce, "Bisa halin musamman na kowane mutum, 'yan kwadago nakasassu 8 suna mukamin tabbatar da ingancin kayayyaki, 'yan kwadago nakasassu 41 suna mukamin kera kayayyaki, sauran 'yan kwadago nakasassu 6 suna mukamin taimakawa."

Nakasassu da yawa sun gaya wa wakilinmu cewa, suna jin dadi sosai ga aikin da suke yi a wannan masana'antu sabo da suna tsammani wannan masana'anta tana bukatarsu. (Sanusi Chen)


1 2