|
|
|
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
|
|
|
|
|
|
(GMT+08:00)
2008-09-15 16:36:07
|
|
Hira da wakiliyar gidan rediyonmu ta yi da Amadou, 'dan wasa daya kawai na kasar Nijer da ke a wasannin Olympics na nakasassu
cri
Amadou da malamarsa, Tsaallah ta dauka wannan hoto Yanzu, ana yin wasannin Olympics na nakasassu na shekarar 2008 a nan birnin Beijing, kasar Nijer ta aika da wata kungiya a wannan gagarumin wasannin. Ko da ya ke akwai 'dan wasa daya kawai a cikin kungiyar wakilai ta kasar Nijer, shi ne kuma Zakari Amadou, amma ya yi alfahari sosai kan wakiltar kasarsa a wasannin Olympics na nakasassu na Beijing. Kwanan baya, wakiliyarmu ta kai ziyarar musamman ga Amadou, yanzu kuma ga hirar da ta yi da Zakari Amadou.
Wanda ke yi wannan magana cike da imani shi ne, Zakari Amadou, 'dan wasa daya kawai da ke cikin kungiyar motsa jiki ta nakasassu ta kasar Nijer. A matsayinsa na wakili daya kawai na 'yan wasa nakasassu na Nijer, Amadou, 'dan shekaru 33 zai shiga wasan daukan nauyi na ajin kilo 67.5 na maza a wasannin Olympics na nakasassu na Beijing.
Wannan ne a karo na farko da Amadou ya shiga wasannin Olympics na nakasassu, kuma shi kadai ne ke wakiltar kasarsa a wasannin, saboda haka, ya san yadda zai sauke babban nauyin da ke bisa wuyansa. Idan ya samu sakamako mai kyau a gasar, to, jama'ar kasar Nijer, wadanda yawansu ya kai miliyan 13 za su yi alfarma kan wannan. A karkashin wannan babban matsi, Amadou ba ya ce, "Babu damuwa, lallai na shirya sosai kan wannan."
Imanin da Amadou ke da shi ya fito ne daga hanyar da yake bi a zaman rayuwarsa cikin dogon lokaci. Tun daga lokacin yarantakarsa, Amadou da ya nakasa a sakamakon ciwon shanyewar jiki ta jariri, ya san ma'anar dogaro da kai, nakasar jiki ba ta hana wannan saurayi samu cigaba ba.
Amadou na da abokai da yawa, ciki kuwa akwai mutane masu koshin lafiya da dama, ya soma wasan daukan nauyi ne a sanadiyar yin cudanya da wadannan abokai masu lafiya. A shekaru 8 da suka wuce, wani abokinsa ya ba shi shawarar daukan nauyi, daga baya kuma, sai Amadou ya haye wahaloli daban daban, ya tsaya kan wasan daukar nauyi, kuma kullum yana iya samun goyon baya da taimako daga abokansa.
Kasar Nijer kasa ce mai fama da talauci, saboda haka, 'yan wasa nakasassu su kan sha wahaloli da dama a fannonin zaman rayuwa, da horo, da kuma shiga wasanni, amma Amadou bai karya ba. Amadou ya yi alfahari sosai da wakiltar kasarsa don a wasannin Olympics na nakasassu.
|
|
|