Aminai 'yan Afrika, kamar yadda kuka san cewa, a yanzu haka dai, ana nan ana gudanar gagarumar gasar wasannin Olympics ta Beijing a shekarar 2008. Amma ko kuna sane cewa, tuni wassu kafofin yada labaru na kasashen duniya, musamman ma jaridun ketare da ake bugawa cikin harshen Sinanci sun kebe shafunansu na musamman domin bayar da labarai a game da gasar wasannin Olympics ta Beijing a shekarar 2008 yayin da suke nuna kyakkyawan fatan alheri ga wannan gagarumar gasa a madadin Sinawa da kuma Sinawa 'yan kaka-gida dake wurare daban-daban na duniya.
Jaridar da ake kira 'Dongfang Shibao' ta Japan, wata jarida ce da ta yi kaurin suna a kasar, wadda take da dadadden tarihi na shekaru goma sha biyar da ake bugawa ciki harshen Sinanci. An labarta cewa, a duk tsawon lokacin da ake gudanar da gasar wasannin Olympics ta Beijing, wannan jarida takan kebe shafunan musamman guda shida a kowane kundinta domin bayar da labarai kan gagarumar gasar daga dukkan fannoni. Ban da wannan kuma, jaridar ' Dongfang Shibao' ta bude layin musamman a game da gasar wasannin Olympics ta Beijing ta hanyar yin amfani da tashar internet dake da lakabi haka : ' Tafe da kyakkyawan mafarki' da kuma tashar internet ta salula dake aiki da Japananci da kuma Sinanci. A yanzu haka dai, wannan jarida takan bayar da labarai da dumi-duminsu cikin sa'o'i 24, hakan ya ba wa Sinawa dake zaune a wurin damar kusantar gasar wasannin Olympics da ake gudanarwa a nan Beijing.
A wata hirar da shugaban kamfanin buga jaridar ' Dongfang Shibao' ta Japan Mista He Yiyun ya yi tare da wakilinmu ta wayar tarho ya furta cewa, har kullum wannan jarida na rike da tasirin da take yi a cikin Sinawa dake zaune a kasar Japan da kuma wassu manyan mahukunta a kasar ta Japan. Mista He ya kuma ce, a cikin yunkurin da ake fito da sabbin shafunan musamman na jaridar a game da gasar wasannin Olympics ta Beijing, sun samu goyon baya daga ministan harkokin waje na kasarsu. Yana mai cewa : 'Gasar wasannin Olympics da ake gudanarwa a Beijing ta kasance wani babban lamari ne da al'ummar kasar Sin ba ta taba gamuwa da shi ba har na tsawon shekaru 100. Mun kebe shafunan musamman guda shida a cikin jaridar domin bayar da labarai kan gasar wasannin Olympics ta Beijing daga dukkan fannoni ; A lokaci guda, mun yi tuntubar ministan harkokin waje na Japan, inda ta jaridarmu ne ya rubuta babbakun fatan alheri ga gasar wasannin Olympics ta Beijing yayin da yake fatan kyakkyawar sa'a ta tabbata ga kasar Sin'.
Tare da ake samun saurin bunkasuwar tattalin arziki a kasar Sin, a yanzu haka dai, Sinawa masu tarin yawa dake zaune a kasar Japan da kuma dimbin aminai Japanawa suna zura ido kan kasar Sin. Fannin tattalin arziki, da al'adu da kuma na wasan motsa jiki da dai sauran fannoni sun fi janyo hankulan wassu masu karantawar jaridar din. Lallai gasar wasannin Olympics ta Beijing ta kara kusantar da Sinawa dake zaune a duk fadin duniya. Mista He Yiyun ya kara da cewa : ' Wassu muhimman abubuwan da muka fi mayar da hankali a kai yayin da muke bayar da labarai dangane da gasar wasannin Olympics ta Beijing a wannan gami, sun hada da makin da wassu 'yan wasa na babban yankin kasar Sin, da yankin Taiwan da kuma na yankin Hongkong domin a karo na faro ne al'ummomin kasar Sin suke taruwa gu daya a kan yankin kasar. Ban da wannan kuma, muna fatan kungiyar 'yan wasa ta kasar Japan za ta samu maki mai kyau a gun gasar da yake muna zaman rayuwa da kuma aiki a kasar ta Japan.'
Mista He ya gaya wa wakilinmu cewa, za mu bayar da wassu muhimman labarai cikin sa'o'i 24 a game da gasar wasannin Olympics ta Beijing ; Ban da wanann kuma, za mu shirya wassu 'yan kallo Japanawa da kuma Sinawa dake zaune a Japan domin kallon gasannin da kungiyar 'yan wasan kasar Sin da kuma ta Japan sukan yi tsakaninsu da sauran kungiyoyin 'yan wasa na ketare.
A karshe dai, Mista He Yinyun ya fada wa wakilinmu cewa, nan gaba za su kara yin hadin gwiwa tare da gidan CRI a fannin bayar da labarai, ta yadda za su kara taka muhimmiyar rawa wajen inganta huldodin dake tsakanin kasashen Sin da Japan. Mista He ya nuna kyakkyawan fatan alheri ta gidan CRI ga gasar wasannin Olyimpics ta Beijing. Yana mai cewa : " Sannu, aminai na gida da na waje. Ni ne He Yiyun, shugaban kamfanin buga jaridar 'Dongfang Shibao' ta Japan. A madadin dukannin Sinawa dake zaune a kasar Japan ne, nake fatan kasar mahaifa za ta yi sa'a, wadda kuma za ta gudanar da gasar wasannin Olympics ta Beijing cikin nasara!"( Sani Wang )
|