Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-12 16:15:33    
'Yan kallo na kasashe daban daban sun je filayen wasannin Olympics don gane ma idanunsu kan gasanni masu ban sha'awa

cri

Bayan da aka fara gasanni daban daban na wasannin Olympics a ran 9 ga wata, bi da bi ne 'yan kallo da suka zo daga wurare daban daban na kasar Sin da kuma kasashen ketare suka kwarara zuwa filayen wasa daban daban, don karfafa gwiwar 'yan wasa.

A ran 9 ga wata, a gidan wasa da ke jami'ar koyon ilmin masana'antu na birnin Beijing, an fara gasar wasan Badminton a tsakanin mata daya-daya, kuma 'yar wasan kasar Indonesia, Yuulianti Maria Kristin da takwararta ta kasar Jamus, Schenk Juliane, su ne suka shiga wannan gasa. Gasar na da ban sha'awa sosai, kuma 'yan kallo sun yi ta karfafa gwiwar 'yan wasan biyu.

Gidan wasa da ke jami'ar koyon ilmin masana'antu ta birnin Beijing na iya daukar 'yan kallo kusan dubu 7, kuma yawan 'yan kallo da suka je kallon gasar sun dau kimanin kashi 80%. Wakilinmu ya ga wasu 'yan kallo da suka zo daga kasar Indonesia, wadanda suke rike da tutar kasarsu. A lokacin da 'yar wasan kasar Indonesia ta sami maki, sai nan da nan, suka tashi suka yi ihu. Ashe, su wadannan 'yan kallo sun yiwo kungiya zuwa nan birnin Beijing ne musamman domin kallon wasannin Olympics, kuma daga cikinsu, akwai wani tsoho mai shekaru 80 da haihuwa, wanda ake kiransa Lie Kok Swan. Ya gaya mana cewa, "Ina farin ciki sosai da zuwa kasar Sin, kuma na taba zuwa nan fiye da sau 10. Na fi son zuwa kasar Sin, sabo da mutanen kasar suna da zumunci sosai. Yau da karfe 10 sai na zo nan gidan wasan, musamman domin nuna goyon baya ga Yuulianti. A hakikanin gaskiya, na zo kasar Sin a wannan karo ne musamman domin kallon bikin fara wasannin Olympics, bikin na da kyau kwarai da gaske, na taba zuwa wurare daban daban na duniya, amma ban taba ganin irin wannan biki ba."

A kasar Indonesia, ana daukar kwallon Banminton tamkar kwallo na kasar, sabo da haka, dimbin jama'ar kasar na sha'awar wasan kwallon badminton. Madam Hana Ananda, daya daga cikin wadannan 'yan kallo na kasar Indonesia, ta ce, "Mun taba zuwa wajen wasannin Olympics a biranen Seoul da Atlanta da Sydney da Athens da kuma Beijing. Mijina yana sha'awar irin yanayi na filayen wasa, ba ya son kallon telebijin. Don kasancewarmu a nan filin wasa, muna iya more sha'awar wasan da yin fargaba da yin azama bisa zazzafan halin wasan."

A gun filin wasa na ranar, mun kuma iya ganin 'yan kallo daga kasashen Denmark da Holland da Amurka da dai sauransu. Amma 'yan kallo mafiya yawa a filin sun zo ne daga kasa mai masaukin baki, wato kasar Sin. Malama Yang Jie, wadda ta zo daga birnin Chengdu na kasar Sin, ta je filin wasa tare da danta, musamman domin gane ma idonsa yanayin filin wasa da kuma kuzari na 'yan wasa. Ta ce, "Na yi murna sosai, sabo da wannan wasan Olympic ne, kuma da ma ban taba zuwa ba. Gasar da aka yi dazun nan a tsakanin 'yan wasan Indonesia da Jamus ta yi zafi sosai, kuma ta sha bamban da yadda mu kan kalla a telebijin, wato tamkar mu ma mun sa hannu a ciki. Dazun nan, na yi ta karfafa gwiwar 'yan wasa, musamman ma ganin yadda 'yar wasan kasar Indonesia ta yi kokari ba tare da kasala ba, na ce ma yarona ya kamata ya koyi juriya irinta."

'Yan kallo sun ji irin zafi da sha'awa na wasanni, daga nasu bangaren kuma, 'yan wasa sun sami goyon baya daga wajen 'yan kallo na kasashe daban daban, musamman ma 'yan kallo na kasar Sin.