Ya zuwa ran 11 ga wata ne, aka shiga rana ta 5 da soma gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing. A cikin 'yan kwanakin da suka gabata, 'yan wasa nakasassu sun yi kokari kuma sun samu maki mai kyau, har sun samu martaba domin kasashensu da kansu a cikin gasanni iri iri. A gun gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing, ba ma kawai ana samun lambar yabo mai walkiya ba, har ma yadda 'yan wasa suke yin gasa cikin adalci da bayar da namijin kokarinsu domin neman samun maki mai kyau ya burge mu.
A ran 10 ga wata da dare, Natalia Partyka, 'yar wasan Pingpong ta kasar Poland wadda take da hannu daya kadai ta cimma burinta. A matsayin daya daga cikin wasu 'yan wasa da suka shiga gasar wasannin Olympic ta Beijing da gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing tare, a cikin gasar wasan Pingpong ta ajin na F10, ta lashe 'yar wasa ta kasar Sin, kuma ta samu wata lambar zinariya. A waje daya kuma, a gun gasar wasannin Olympic ta Beijing da aka rufe a kwanan baya, ita da abokan 'yan wasa mata na kasar Poland sun samu maki mafi kyau a kan tarihin kungiyar wasan Pingpong ta mata ta kasar Poland. Sakamakon haka, a cikin wannan lokacin zafi, madam Natalia Partyka ba ta yi bakin ciki ba, kuma yanzu ta riga ta tsara wani sabon burin da take son cimmawa a nan gaba.
"Yanzu ban cimma duk burina ba. Sabo da na shiga gasa ta tsakanin kungiya kungiya kawai, ban samu izinin shiga gasa ta tsakanin mutum dai dai ba a gun gasar wasannin Olympic ta Beijing. Ina fatan zan iya shiga gasa ta tsakanin mutum dai dai da gasa ta tsakanin kungiya kungiya tare a gun gasar wasannin Olympic ta London. A wancan lokaci, zan iya fadi cewa, na cimma duk burina gaba daya. Amma tabbas ne ina da sabon mafarki a wancan lokaci, wato ina fatan zan samu lambar yabo a gun gasar wasannin Olympic."
Kokarin da Natalia Partyka ta yi ya burge duk wanda yake kallon gasar da ta shiga. Xiao Wang wanda yake sha'awa sosai kan wasan Pingpong yana daya daga cikinsu.
"Lokacin da ake gasar wasannin Olympic ta Beijing, ta shiga gasa ta tsakanin kunigya kungiya a madadin kasar Poland. Ta kware sosai kan wanann wasa. Ita ce Partyka. Ta shiga gasar tamkar wani mutum maras nakasa. Ina girmame ta kwarai."
Ba ma kawai ana girmama makin da 'yan wasa nakasassu suka samu ba, har ma ana girmama kokari da ruhun wasannin motsa jiki da suka bayar a cikin gasanni. Alal misali, a cikin gasar wasan ninkayya ta mita 400 ta ajin na S13 da aka yi a ran 8 ga wata, bayan da 'yan wasa nakasassu 7 suka kammala zango mita 50, sun dakatar da gasarsu, kuma sun bar wurin ninkayya cikin dan lokaci. Sun yi haka ne domin Van Roosmalen Teigan, wata 'yar wasa nakasasshiyya ta kasar Australiya wadda ta kamu da ciwon kunne da na ido ba ta iya sauraren umurnin alkali ba.
Mr. Luca Pancalli, shugaban kwamitin kula da wasannin Olympic na nakasassu na kasar Italiya yana ganin cewa, "a gun wannan muhimmin dakalin wasanin motsa jiki, 'yan wasa nakasassu fiye da 400 na kasashe da yankuna daban daban sun nuna fasahohin da suka mallaka, kuma ba za su ji suna matsayin kasa da sauran mutane ba, kuma suna samun nasara da farin ciki tamkar 'yan wasa marasa nakasa suka samu a gun gasar wasannin Olympic. Bugu da kari kuma, ta hanyar nune-nunen halin da 'yan wasa nakasassu suke ciki, muna fatan nakasassu wadanda har yanzu ba su ji farin ciki daga wasannin motsa jiki ba za su iya gane cewa, wasannin motsa jiki za su iya sanya su da su ji dadin zaman rayuwa da zaman al'umma sosai"
'Yan wasa nakasassu da suke gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing sun yi amfani da hankalinsu da iyawarsu da kokarinsu wajen kawar da matsalolin da mutane marasa nakasa ma ba su iya fama da su ba. Wannan kuma ya gaya mana cewa, muddin aka kula da su, kuma aka ba su dama, za su iya bayar da gudummowarsu ga zaman al'ummarmu kamar sauran mutane marasa nakasa. (Sanusi Chen)
|