Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-11 21:25:30    
Sin za ta dauki jerin matakai don daidaita matsalar samun aiki yi dake gaban yankuna da girgizar kasa ta rutsa da su a yankin Wenchuan

cri

An labarta cewa, a yanzu haka dai, an rigaya an shiga matakin sake gina wuraren da bala'in girgizar kasa ya rutsa da su a yankin Wenchuan na lardin Sichuan na kasar Sin. Yau Alhamis, wani babban jami'in sashen kula da harkokin bada tabbaci ga zaman al'ummar kasar Sin, Zhang Xiaojian ya furta cewa, gwamnatin kasar za ta dauki jerin matakai don tallafa wa wadanda wannan mummunan bala'i ya galabaitar da su da zummar samar musu da damar samun aikin yi.

A wata sabuwa kuma an ce, ya zuwa yau da safe da misalin karfe 12, yawan mutanen da suka rasa rayukansu cikin bala'in ya kai 69,226, yayin da wasu 374,643 suka jikkata kuma mutane 17,923 sun bace.

Wani rahoton da aka gabatar ya ce, ya zuwa ranar jiya Laraba, yawan matsugunan wucin gadi da aka harhada ya kai 677,131.

Ban da wannan kuma, ma'aikatar kudi ta kasar Sin ta gabatar da rahoton cewa, ya zuwa yau da safe da misalin karfe 12, yawan kudaden da gwamnatoci na matakai daban-daban na kasar suka zuba wajen yaki da bala'in da yin ceto ya zarce kudin Sin wato RMB yuan biliyan 67 da miliyan 500 ;

Kazalia, mun samu labarin cewa, ya zuwa yau da safe da misalin karfe 12, adadin darajar kudi da kayayyaki da bangarori daban-dazban na ciki da wajen kasar suka bayar ya wuce RMB yuan biliyan 59 da miliyan 300. ( Sani Wang )