Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na Xinhua ya bayar an ce, jami'ar sakatariyar yarjejeniyar hakkin nakasassu ta Majalisar Dinkin Duniya, Madam Ito Akiko ta bayyana a rana jiya cewa, a 'yan shekarun baya, an samu cigaban a-zo-a-gani a fannin bunkasa sha'anin nakasassu a kasar Sin; kana ta furta cewa, tana iya jin yadda gwamnatin kasar Sin take kokarin kiyaye hujjoji da fa'ida na nakasassu yayin da take mayar da aikin bunkasa sha'anin nakasassu a matsayin daya daga cikin muhimman ayyuka da take yi.
Kazalika, Madam Ito Akiko ta fadi cewa, bikin bude gasar wasannin Olympics ta nakasassu cike yake da kyakkyawan halin bayyanuwar al'adu da na fasaha da kuma na zamani. ( Sani Wang )
|