Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-11 17:21:57    
Birnin New York ya shirya biki don tunawa da mutane da suka rasa rayukansu a cikin harin ta'addanci da aka kai a ran 11 ga watan Satumba na shekara ta 2001

cri
Yau wato ran 11 ga watan Satumba, rana ce ta cikon shekaru 7 da faruwar farmakin ta'addanci da aka kai wa birnin New York na kasar Amurka, kamar yadda ta yi a shekarar da ta gabata, gwamnatin birnin za ta shirya wani biki a ran nan bisa agogon wurin domin tunawa da mutanen da suka rasa rayukansu a cikin farmakin. Bisa ka'idar da a kan bi, a ranar da dare, gwamnatin za ta harbi haske sau biyu a sararin sama domin alamanta gine-gine masu tagwaye na cibiyar cinikayya ta duniya, ta yadda mutane za su iya tuna da matattu.

Bisa shirin bikin, Michael Bloomberg, magajin birnin New York shi da fararen hula za su tsaya cik su yi shiru don nuna alhini a karfe 8 da minti 46, da karfe 9 da minti 3, da karfe 9 da minti 59, da kuma karfe 10 da minti 29 na safe a ran 11 ga wata bisa agogon wurin, wadanda su lokuta ne da jiragen sama biyu suka kai farmaki kan gine-gine biyu na cibiyar cinikayya ta duniya da kuma faduwar gine-ginen. Ban da wannan kuma a gun bikin, za a karanta sunayen mutane 2751 da suka rasa rayukansu a cikin harin da aka kai wa gine-ginen.

Ko da yake shekaru 7 suka wuce da faruwar wannan farmakin ta'addanci, amma ya zuwa yanzu wasu 'yan kasar Amurka suna ganin cewa, kamar lamarin ya faru ne a jiya. Ko shakka babu, bikin tunawa da a kan yi sau daya a ko wace shekara ya kan fadakar da mutane kan lamarin mai bakin ciki. Lokacin da ake nuna alhini ga mutanen da suka rasa rayukansu, kullum a kan manta da mutanen da suka jikkata a cikin lamarin. Lokacin da faruwar lamarin, sun yi sa'a sun kubutar da kansu daga hadarin, amma a cikin zaman rayuwarsu na yanzu, sun zama mutane marasa sa'a.

Kafin faruwar farmakin ta'addanci a ran 11 ga watan Satumba, Madam Lauren Manning da ke gudanar da aikinta a titin Wall tana kan matsayin koli wajen aikinta, amma zaman rayuwarta ya canja daga waccan rana. Sabo da rauni mai tsanani da ta samu sakamakon gobara, ta kwanta a asibiti har makwanni da dama, bayan watanni da dama, an sallame ta daga asibiti. Yanzu ko a lokacin zafi, ba yadda za a yi sai ta sanya dogon tufafi. Kuma ba ta iya yin yawo tare da karamin karenta kamar yadda ta kan yi a da ba, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da ba ta iya jure wahalar yayin da karen ke gudu ba. Har ma ba ta iya dafa abinci don iyalanta, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da fatarta za ta kumbura ko gamuwa da mai mai zafi dan kadan.

Ana iya samun dimbin mutane masu jin raunuka kamar Madam Manning, ya zuwa yanzu babu ainihin adadinsu ba. Lokacin da dimbin mutane suka fara manta da wannan farmakin ta'addanci, illar da ya kawo wa masu jikkata za ta dade za ta kansace a cikin dukkan zaman rayuwarsu.

Ban da mutanen da suka ji raunuka kai tsaye, mazaunan birnin New York da ke da zama a wuraren da ke kusa da cibiyar cinikayya ta duniya su ma sun sha wahaloli sosai a duk fannonin jiki da kuma tunani a cikin shekaru 7 da suka gabata. Wani biciken ilmin likitanci ya bayyana cewa, a cikin watanni 10 da faruwar wannan farmakin ta'addanci, a kalla rabin mutane da suka ganam ma idonsu kan lamarin sun kamu da cututtukan numfashi, mutane masu dimbin yawa daga cikinsu kuma sun gamu da matsalar tunani. Manazarta sun gano sinadarai masu haddasa sankara a cikin kangaye da kuma abubuwan da suka fadi daga sararin sama. Kuma sun bayyana cewa, illar da wadannan munanan sinadarai suka yi wa jikin dan Adam ba za ta bullo ba sai dai bayan shekaru da dama.(Kande Gao)