Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-11 15:14:29    
Labaru masu ban sha'awa na kasar Sin

cri

A cikin shirinmu na yau za mu kawo muku wasu labaru masu ban sha'awa,muna fatan za ku ji dadin labarum.

Wani dan sanda ya cika alkawarinsa. An samu wani dan sanda mai suna Sun Zongqun a birni Wuhan na lardin Hubei dake tsakiyar kasar Sin da ya kula da wata yarinya mai shekaru tara.wannan yarinya ba tasa ba ce, ta wani mai laifin da aka yanke masa hukuncin kisa.Sunan mai laifi Hu Ming ya kai hari kan wani aboki na matarsa a da da kashe abokansu biyu domin ba su ari masa kudi ba.Bayan da aka yanke masa hukuncin kisa, Hu ming ya durkusa a gaban dan sanda ya roke shi da ya kula da diyarsa bayan aka sanya shi gidan lahira. Dan sandan ya dau alkawari. Bayan mutuwarsa,sai dan sanda Sun Zongqun ya cika alkawarinsa yana kula da yarinta.

Ma'aikatan hukuma sun rufe wani kantin day a tanadi takardun jabu. A ranar laraba da ta shige.wata mata mai suna Cai a birnin Wuhan na lardin Hubei na kasar Sin ta zo wani reshen ofishin kula da masana'antu da kasuwanci na birnin, ta sanar da ma'aikatan ofishin cewa danta mai shekaru tara dake karatu a makarantar firamare Nan Wangshan ya saye wata takardar shaida daga wani kaniti kusa da makarantarsa. Da samun labarin,ma'aikatan ofishin sun je wurin ba tare da bata lokaci ba,da isowarsu sun gano sauran takardun jabu barkatai.nan da nan sun rufe kantin da kai mai tafiyar da harkokin kanti ofishinsu domin bincike.

Wani manomi ya yi karatu tare da 'ya'yansa biyu. An samu wani manomi mai suna Chen Rongli wanda ya ke da shekaru 39 da haihuwa a wurin Changjiang na lardin Hainan dake kudancin kasar Sin.Bayan ya yi shekaru tara yana karatu kwanakin baya makarantar koyon ilimin noma ta Hainan ta shiga da shi inda 'ya'yansabiyu suna karatu a ciki. Chen ya bar makaranta ne saboda talauci,duk da haka ya niyyata zai koma makaranta,a ganinsa ilimi na iya canza rayuwa. A shekara ta 2001 ya dawo makaranta,A watan Yuni na wannan shekara ya shiga jarrabawar neman shiga manyan makarantu a kasar Sin,bai yi sa'a ba ya gaza. Da ganin haka shugaban makarantar koyon ilimin noma ta Hainan ya tsai da kudurin daukarsa a makaranta domin ya koyi ilimin noma.Da samu damar karatu,farin ciki ya rufe shi. Ya ce da ya kammala karatunsa zai yi amfani da ilimin da ya samu wajen bunkasa noma.

Wani maras lafiya ya rubuta littafi don yaba matarsa.

An sami wani tsoho da ke fama da cutar inna cikin shekaru 22 da suka shige mai yawan shekaru 68 da haihuwa a birnin Haikou na lardin Hainan dake kudancin kasar Sin.A ranar laraba da ta wuce ya kammala littafinsa mai suna Huangshan Yeling. A cikin shekara daya da rabi,ya yi aiki dare da rana ya rubuta labarai kan yadda matarsa ta kula da shi cikin shekaru 22 bayan da inna ta shanye shi.Tsohon ya ce "ina so in rubuta wani littafi domin murnar kaunar dake tsakaninmu.lalle wannan littafi ya isa abin godiya ga matarsa.

Ba a gabatar da shi a gaban kotu ba. An sami wani dan makararn senior middle school mai suna Chen jiang a wurin Pengzhou na lardin Sochuan dake tsakiyar Sin ta yamma. Bayan da kekensa na hawa ya bace,sai ya yi satar kudi domin biyan kudin diyya saboda keke ba nasa ban e,ya yi aro ne daga wani abokinsa,da yake satar kudin an kama shi.ya amsa laifinsa .ofishin 'yan sanda ya bukace shi da ya zama a gida.A ran 12 ga watan Mayu,an yi girgizar kasa mai tsananni a garinsa,wannan dan makaranta ya nuna bajinta wajen ba da taimako ga saurana mutanen da suka sha wahalar girgizar kasa,har ma ya ba da babban taimako ga wurin da yake zama a ciki.Daga baya ofishin 'yan sanda ya tsaida kuduri cewa ba a gabatar da shi a gtaban kotu ba.