Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-11 15:03:36    
Masu aikin tausa makafi, wadanda suke kaunar bayar da hidima ga gasar wasannin Olympics ta nakasassu

cri

Bayan da aka kammala gasar wasannin Olympics ta Beijing cikin nasara, za a maraba da gasar wasannin Olympics ta nakasassu a karo na 13 a nan birnin Beijing. A lokacin, 'yan wasa nakasassu fiye da 4000, da masu horar da 'yan wasa da alkalan wasa sama da 2500, da kuma masu aiki a kafofin watsa labaru fiye da 4000, wadanda za su zo daga kasashe da shiyyoyi 148, za su taru a nan birnin Beijing. Yanzu, masu hidima na sa kai na gasar wasannin Olympics ta nakasassu da yawansu ya kai dubu 44 suna shan aiki, don tabbatar da shirya gasar wasannin Olympics ta nakasassu kamar yadda ya kamata. Daga cikinsu kuma, akwai wasu mutanen musamman, su ne masu aikin tausa makafi. Yanzu, ga cikakken bayanin da wakilinmu ya ruwaito mana.

A cibiyar shakata ta asibitin da ke kauyen wasannin Olympics na nakasassu, akwai masu aikin tausa da yawansu ya kai kusan 60 suna bayar da hidimar tausa irin na likitancin gargajiyar kasar Sin ga 'yan wasa, da jami'ai, da manema labaru, da kuma abokai daga kasashe daban daban, ciki kuwa wadanda guda goma su ne makafi. Lu Xin yana daya daga cikinsu. Ya gaya wa wakilinmu cewa,

"Aikin tausa iri na likitancin gargajiyar kasar Sin, wata sana'a ce mai halin musamman na kasar Sin. Yana da amfani mai ban mamaki, kuma ba tare da kawo illa ba. Wato a kawar da gajiya, har ma yin jiyya ta hanyar tausa, lallai ba a iya samun wannan aiki a kasashen ketare. A ganina, na iya zaman wani mai aikin sa kai, wannan abin alfahari ne, saboda na iya yin amfani da wannan dama don nune nunen likitancin gargajiyar kasar Sin, da fasahar tausa irin ta kasar Sin ga duniya."

Lu Xin, 'dan shekaru 26 ya fito daga birnin Wuhan na lardin Hubei, yana aikin tausa har shekaru 6. A lokacin shekarun haihuwarsa na 19, yana karatu a aji na farko a jami'a, amma tun daga lokacin kuma, zaman rayuwarsa ta samu canjawa a sakamakon ciwon idanu. Ya soma koyon fasahar tausa ta makafi a maimakon fasahar likitancin yamma. A 'shekaru shida da suka wuce, Lu Xin ya zo nan birnin Beijing, kuma har zuwa yanzu yana aiki a wani asibitin tausa. Lu Xin bai rasa amincewa kan zaman rayuwarsa ba, a sanadiyar ciwon idanu da ya samu. Ya gaya wa wakilinmu cewa,

"A ganina, ra'ayin da mutane ke nuna kan zaman rayuwa na da muhimmanci sosai. Ko da ya ke na samu ciwon idanu, amma tilas ne na fuskanci wasu matsaloli, kamar misali, na kan yi iyakacin kokarina don yin abubuwan da nake iyawa. Ko shakka babu, muna son samun taimako daga sauran mutane, ta yadda za mu samu kauna daga zaman al'umma, kuma muna godiya ga zaman al'umma."

Daraktan cibiyar ba da jagoranci kan tausa makafi ta birnin Beijing Mr. Wang Changhan ya gaya wa wakilinmu cewa, kwamitin shirya wasannin Olympics na Beijing na fata wasu masu aikin tausa makafi za su yi aiki a kauyen wasannin Olympics na nakasassu a lokacin gasar wasannin Olympics, da ta nakasassu, saboda haka, masu aikin tausa makafi da yawansu ya wuce 500 a nan birnin Beijing sun yi rajista. Bisa bukatun kwamitin shirya wasannin Olympics na Beijing, an zabi mutane 10 daga cikinsu. Darakta Wang Changhan ya ce, wadannan makafi sun gamu da wasu wahaloli a fannonin karatu, da samun aikin yi, da kuma yin cudanya, amma a karkashin taimakon da bangarori daban daban suka yi masa, yanzu suna iya zama da aiki kamar yadda ya kamata. Ya yaba wa wasannan masu aikin tausa cewa,

"Makafi na zamani su ne samari masu ilmi, da al'adu, da ra'ayoyi, kuma kamar sauran mutane masu lafiyar jiki suna ba da taimakonsu ga zaman takewar al'umma."

Masu aikin tausa makafi da ke asibiti na kauyen wasannin Olympics na nakasassu su ne samari. Chen Huiying, 'yar 26 daga birnin Beijing. Ta gaya wa wakilinmu cewa, tana iya aiki a asibitin tausa na birnin Beijing, wannan abin sa'a ne gare ta. A lokacin da kwamitin shirya wasannin Olympics na Beijing ya tsaida kudurin zaben masu aikin tausa makafi, nan da nan ta yi rajista. Bayan da aka yi zabe har sau da yawa, a karshe dai ta samu nasara, wannan kuma ya karfafa imaninta.

"Kafin aka zabe mu masu aikin sa kai, za a yi mana jarrabawa ta fuska da fuska, da ta muhimman ilmi. Da farko, tilas ne muna da isasshen ilmi kan wasannin Olympics, bayan haka kuma, muna iya harsunan waje, don ba da sauki wajen yin mu'ammala. Mun riga mun samu horo da kuma yin shirye-shirye kan wannan."

Saboda tana iya Turanci sosai, don haka, ta samun aikin yi a kauyen wasannin Olympics na nakasassu, inda tana iya yin cudanya da 'yan wasa, da jami'ai, da manema labaru daga kasashe daban daban na duniya. Chen Huiying ta gaya wa wakilinmu cewa,

"Bayan da na yi musu jiyya, sai suka samu sassautar jikinsu, gaskiya ne sun gamsu da wannan, kuma sun yi godiya ga hidimar da muka bayar. Gaskiya ne mun yada fasahar gargajiyar kasar Sin ga dukkan duniya, ina jin alfahari sosai."