Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-10 17:34:27    
Har zuwa yanzu ba a warware halin kaka-ni-ka-yi kan siyasa da ake ciki a kasar Zimbabwe ba

cri

Ran 8 ga wata, Mr. Thabo Mbeki shugaban kasar Afirka ta kudu ya sake kai ziyara ga kasar Zimbabwe, ya yi kokari na karshe domin warware halin kaka-ni-ka-yi da ake fuskantar da shi cikin shawarwarin rarraba iko tsakanin bangarori dabam daban. Amma har zuwa ran 9 ga wata da dare, ba a sami cigaba ba, bangarorin dabam daban ba su sami ra'ayi iri daya ko kadan kan batun rarraba ikon mulki.

A karkashin sulhun tawar da Mr. Mbeki ya yi, bangarori uku na shawarwarin rarraba ikon mulki, wato Mr. Mugabe shugaban kasar Zimbabwe kuma shugaban jam'iyyar Zanu-PF wanda ke kan karagar mulkin kasar Zimbabwe, da Mr. Tsvangirai da Mr. Mutambara shugabanni na rukunai biyu na jam'iyyar MDC wadda ita ce jam'iyyar adawa sun halarci shawarwari.

Bayan shawarwarin da aka yi, Mr. Mugabe ya nuna cewa, ko da yake har zuwa yanzu, ba a daddale ko wane irin yarjejeniyar rarraba ikon mulki tsakanin bangarori dabam daban ba, amma za a cigaba da yin shawarwari, wannan shi ni wani shawarwari mai kyau. Mr. Chamisa kakakin rukunin Tsvangirai na jam'iyyar MDC ya ce, yanzu ana cigaba da yin shawarwari. Kuma bangarori dabam daban suna neman ra'ayi iri daya, ko da yake akwai kasancewar sabanin ra'ayi sosai, amma suna kokarin warware wannan matsala. Mr. Mutambara wani shugaba na rukuni daban na jam'iyyar MDC ya nuna cewa, ko da yake ana kasancewa cikin rikici sosai, amma yana da kyakkyawan fata ga makomar shawarwari.

Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Zimbabwe ya ce, a kalla dai shugaba Mbeki na kasar Afirka ta kudu zai yi kwanaki biyu a kasar Zimbabwe, kuma zai yi shawarwari tare da shugabannin bangarori dabam daban. Kafin wannan, kungiyar tarrayar raya kasashen da ke kudancin Afirka, wato kungiyar SADC ta bukaci Mr. Mbeki ya yi sulhuntawa domin warware halin da ake ciki a kasar Zimbabwe. A watan baya, bayan da aka yi taron shekara-shekara na kungiyar SADC a kasar Afirka ta kudu, Mr. Mbeki ya zamar shugaban kungiyar na wannan zagaye. Saboda haka, warware rikicin siyasa a kasar Zimbabwe, da kuma sanya bangarori dabam daban su cimma yarjejeniyar rarraba ikon mulki ya zama wani muhimmin aiki na kungiyar SADC. Mr. Mbeki ya sake kai ziyara ga kasar Zimbabwe domin neman cimma wannan aiki.

An fara yin shawarwari tsakanin bangarori dabam daban baya sun daddale takardar tunatarwar fahimtar juna a ran 21 ga watan Yuli na shekarar da muke ciki. A cikin tsawon lokaci fiye da wata guda, an yi shawarwari da dama, kuma sun sami ra'ayoyi iri daya kan batutuwa 13 da ke cikin dukkan batutuwa 14, amma sun shiga halin kaka-ni-ka-yi kan batu mafi muhimmanci na karshe na rarraba ikon mulki. Abu mafi muhimmanci shi ne jam'iyyar MDC wadda ta zama jam'iya mafi girma cikin sabuwar majalisar kafa dokoki ta ki amincewa shugaba Mugabe ya cigaba da sarrafawa harkokin tsaro na kasar Zimbabwe. A kwanakin baya, Mr. Mugabe ya nuna cewa, idan shugaba Tsvangirai na jam'iyyar MDC ba ya sa hannu kan yarjejeniya, zai gefentar da jam'iyyar adawa, zai kafa majalisar ministoci kai tsaye. Game da haka, Mr. Tsvangirai ya ce, idan ba a iya warware halin kaka-ni-ka-yi da ake ciki a yanzu, ya kamata a sake yi babban zabe a karkashin idanun kasashen duniya.

Masu bincike suan ganin cewa, Mr. Mbeki ya sake kai ziyara ga kasar Zimbabwe a daidai lokacin da bangarori dabam daban na kasar ke da rikici mafi tsanani. Idan ba za su iya daddale yarjejeniya, har ma sake yin babban zabe, sai za a koma baya, kokarin da aka yi zai zama shirme, shugabannin kungiyar SADC ba su son wannan sakamako. Saboda haka, ana iya yin kiyasta cewa, Mr. Mbeki zai yi kokarin sanya bangarori dabam daban su sami ra'ayi iri daya kuma gefentar da sabannin ra'ayi domin neman samun dabarar warware halin kaka-ni-ka-yi da ake ciki.