Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-10 15:07:50    
Abubuwa uku masu ban mamaki da aka samu bayan lambar zinariya ta farko da aka samu wajen gasar daukar nauyi ta wasannin Olimpic na nakasassu

cri

Jiya da yamma, an bayar da lambar zinariya ta farko wajen gasar daukar nauyi ta wasannin Olimpic na nakasassu na Beijing na shekarar 2008 a dakin wasan motsa jiki na jami'ar koyar da ilmin zirga-zirgar jiragen sama ta Beijing . Abin mamaki da ya faru shi ne,dan wasan kasar Nigeriya da ke cikin rukunin B mai suna Ruel Ishaku ya sami wannan lambar , amma ba hakan kawai da aka yi ba, sai kuma bayan lambar , an boye da abubuwan mamaki guda uku.

Wanda ya sami lambar zinariya a gun gasar wasannin Olimpic ta nakasassu shi ne dan wasan kasar Nigeriya.

A ranar 9 ga wannan wata da yamma, an kawo karshen gasar daukar nauyi bisa aji na kilo 48 na maza nakasassu na wasannin Olimpic na shekarar 2008 a dakin wasan motsa jiki na jami'ar koyar da ilmin zirga-zirgar jiragen sama ta Beijing , dan wasan kasar Nigeriya mr Ruel Ishaku ya ci lambawan, kuma ya karya matsayin bajinta na duniya don nauyin da ya dauka ya kai kilo 169. Dayake kafin gasar, Ruel Ishaku ya yi rajistar shiga gasar da ke tsakanin 'yan wasa na rukunin B, wato a ce, in dan wasa ya yi rajistar shiga gasar da ke tsakanin 'yan wasa na rukunin B, to ana iya cewa, sakamakon da dan wasan ya samu a da ya yi baya ke nan, amma Ruel Ishaku ya fito a gaba , kuma ya sami lambar zinariya, abin nan ne da ba a kan samunsa ba ko a wajen gasar wasannin Olimpic ko a wajen gasar wasannin Olimpic na nakasassu. Ana iya cewa, Mr Ruel Ishaku ya kago wani abin mamaki gare mu, bayan gasar, ya karbi ziyarar musamman da manema labaru suka yi masa, ya bayyana cewa, abun da na ji mai kyau ne sosai, makasudina na farko shi ne, zuwa birnin Beijing don shiga gasar wasannin Olimpic ta nakasassu kawai, amma yanzu, ba ma kawai na sami lambar zinariya ba, hatta ma na karya matsayin bajinta na duniya. A gaskiya dai, na cim ma burina.

Game da abun mamaki na biyu, Mr Ruel Ishaku ya gaya wa manema labaru cewa, a cikin wani horon da aka yi masa a shekarar 2007, ya ji rauni sosai, malaman koyarwarsa da likitan kungiyarsa sun gaya masa cewa, ba zai iya samun damar shiga gasar wasannin Olimpic ta nakasassu ta shekarar 2008 ta Beijing ba, amma Ruel Ishaku bai amince da wannan ba, ya nace ga ci gaba da shiga horon da aka yi masa. Ya bayyana cewa, a shekarar bara, na taba gamuwa da wata matsala . A watan Augusta na shekarar bara, sandar wasa da aka yi da karfe mai nauyi kilo 125 ya fadi a kan kirjina, wannan ya kawo mini illa sosai, amma ban tsaya ba, na ci gaba da rike da niyyata , sa'annan kuma na sami sauki da kyau,kuma na sake shiga horon da aka yi mini a watan Janairu na shekarar da muke ciki.

Abun mamaki na uku shi ne, bisa matsayin nakasasshen da kafofinsa ya shanye sosai , Ruel Ishaku ya yi zaman rayuwa cikin faranta rai a kowace rana, yana kokari ba tare da kasala ba, a karshe dai ya shiga gasar wasannin Olimpic ta nakasassu, kai, abin nan abun mamaki ne ba shakka.

Mr Ruel Ishaku ya gaya wa manema labaru cewa, ya nuna godiya sosai ga 'yan kallon kasar Sin da suka yi masa tafi tare da kirari, duk saboda 'yan kallo sun kara masa kuzari. Ya ce, a gaskiya dai, na ji abun da aka yi mini sosai, ba masu nuna goyon baya na kasarmu Nigeriya kawai suka yi ba, 'yan kallo da yawa na kasar Sin su ma sun yi mini kirarin kara mai, sun ba ni karfin bajinta sosai.(Halima)