Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-10 15:03:46    
Shiyyar wasannin Olympics dukiya ce da gasar wasannin Olympics ta Rome ta bayar

cri

A shekara ta 1960, an shirya gasar wasannin Olympics ta karo na 17 a birnin Rome, babban birnin kasar Italiya. Lokacin da ake gina filaye da dakuna da kuma kayayyakin wasannin Olympics, gwamnatin kasar Italiya ta dora muhimmanci sosai kan hada kayayyakin wasannin Olympics da tsare-tsaren birnin tare. Yau da rabin karnin da ya gabata, ana yin amfani da wadannan kayayyakin wasannin Olympics, ta haka 'yan birnin Rome suna iya kara jin dadin zaman rayuwarsu. To yanzu ga cikakken bayani.

Daniel Modigliani, shugaban hukumar tsare-tsaren birnin Rome kuma mai zayyane-zayyane kan gine-gine ya bayyana cewa, gasar wasannin Olympics ta Rome ta shekara ta 1960 ta canja tsarin birnin Rome, da kuma kaddamar da shirin raya kayayyakin wasannin motsa jiki a cikin unguwoyi daban daban na birnin. Kuma ya kara da cewa,

"Ya zuwa yanzu wasu muhimman ayyukan yau da kullum da aka raya a wancan lokaci suna takawa muhimmiyar rawa. Kuma wani sakamako mai kyau da aka samu daga wasannin Olympics na Rome shi ne an samu kusan dukkan kayayyakin wasannin Olympics na wancan lokacin ne daga hannayen sanannun masu zayyane-zayyane kan gine-gine, wadanda har yau ake mayar da su a matsayin gine-ginen zamani mafi kyau, kamar kauyen 'yan wasannin Olympics na Rome."

Bayan da aka kammala gasar wasannin Olympics ta Rome, an sayar da kuma bayar da hayar dakunan kwana da ke kauyen 'yan wasannin Olympics ga ma'aikatan gwamnatin kasar Italiya. Daga baya kuma bisa dukkan tsare-tsaren birnin Rome, an gina wurin shan iska na wake-wake a wurin da ke kusa da kauyen domin kara abubwan al'adu a cikin dakunan kwana da ke da halin musamman na fasahar zamani, inda ya zuwa yanzu a kan shirya bikin nuna filim na kasa da kasa na Rome da a kan yi a ko wace shekara da kuma bikin nune-nunen tufafi na Rome da a kan yi domin samun sabbin mutane masu sanya tufafin da ake nunawa.

Ban da kauyen 'yan wasannin Olympics, filaye da dakunan wasannin motsa jiki yana da muhimmanci sosai game da ko wanen birnin da ya taba daukar nauyin shirya wasannin Olympics. Mr. Modigliani ya bayyana cewa, muhimman filaye da dakunan wasannin motsa jiki da aka gina don gasar wasannin Olympics ta Rome suna cikin yankin kayayyakin motsa jiki na zamani da ke arewacin birnin Rome. Kuma ya kara cewa,

"A da akwai wasu kayayyakin wasannin motsa jiki a wancan wuri, kamar filin wasannin motsa jiki da kuma wurin ninkaya da dai sauransu. Amma domin wasannin Olympics, an sake gina wadannan kayayyaki, a waje daya kuma an gina babban gini na wasannin motsa jiki da kuma filin wsannin motsa jiki na Flamino da dai sauran kayayyakin ba da hidima da ke kewayensu."

Game da gasar wasannin Olympics ta Beijing, Mr. Modigliani shi ma ya bayar da shawararsa. Ya ce,

"A ko wane karo da muka samu damar shirya gasanni na duniya, ya kamata mu yi la'akari da yadda za a ba da wasu kayayyakin tarihi da ke da ma'ana ga birane. Kuma ina fatan birnin Beijing zai iya gudanar da harkoki bisa wannan ra'ayi. Shawarata ita ce ya kamata birnin Beijing ya yi amfani da wannan damar shirya wasannin Olympics wajen gina wani tsarin zirga-zirga na jama'a, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da wannan shi ne abin da muka kasa samuwa daga wajen gasar wasannin Olympics ta Rome."(Kande Gao)