Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-10 15:02:01    
'yan wasan kasashe daban daban na duniya suna shiga horon da aka yi musu cikin tsanani don neman samun sakamako mai kyau

cri

Jama'a, yanzu ga shirinmu na makon jiya dangane da manyan labarun wasannin Olimpic.Yau za mu kawo muku wani bayanin da ke da lakabi haka: 'yan wasan kasashe daban daban na duniya suna shiga horon da aka yi musu cikin tsanani don neman samun sakamako mai kyau.

A ranar 25 ga wannan wata, a lokacin da ya rage makonni biyu don soma bikin bude gasar wasannin Olimpic ta Beijing, kungiyar wakilan 'yan wasan kasar Sin da za ta halarci gasar wasannin Olimpic ta Beijing ta kafu a nan Birnin Beijing. Kungiyar ita ce kungiyar wakilan 'yan wasan kasar Sin da 'yan wasanta mafi yawa suka shiga gasannin wasanni mafi yawa a tarihin halartar gasar wasannin Olimpic. Mataimakin shugaban kungiyar Mr Duan Shijie ya bayyana cewa,

Kungiyar tana kunshe da mutane 1099, wadanda za su halarci dukkan manyan ayyuka 28 na gasannin wasannin Olimpic na Beijing da rassa gasanni 38. Kungiyar kuma tana kunshe da 'yan wasa da yawansu ya kai 638, daga cikinsu, 'yar wasan tsallake cikin ruwa mai suna Guo Jingjing da dan wasan harbe-harbe Mr Tan Zongliang da dan wasan kwallon kwando Mr Li Nan dukkansu sun taba shiga cikin gasannin wasannin Olimpic na Atlanta da na Sydney da na Athens, sauran 'yan wasa da yawansu ya kai 469 sun shiga gasannin Olimpic ne a karo na farko.

Kodayake kungiyar kasar Sin ba ta nuna fin karfi sosai ba, wato ba ta ce za ta sami lambobin yabo nawa gare ta ba a wannan karo, amma wadanda suka zo daga kasashen waje sun bayyana cewa, mai yiyuwa ne 'yan wasan kasar Sin za su sami lambobin zinariya wajen gasannin wasannin tsallake cikin ruwa da daukar nauyi da harbe-harbe da lankwashe jiki da kwallon tebur da sauransu. A fuskar karfin da kasa mai daukar nauyin shirya gasannin take da shi a hakika, kungiyoyin wakilan 'yan wasan kasashe daban daban na duniya suna nan suna gaggautawar yin horonsu kafin soma gasannin.

'Yan wasan kasashen kudu maso gabashin Asiya suna neman samun lambobi a tsakaninsu a kodayaushe. Kasar Indonesiya da Thailand da Malasiya za su tura 'yan wasansu da ke da karfin yin takarar samun lambobi zuwa gasannin Olimpic na Beijing. Kasar Indonesiya za ta tura 'yan wasa 11.

Kwamitin wasannin Olimpic na kasar Amurka ya bayar da sunayen 'yan wasa da ke cikin kungiyarta, daga cikinsu da akwai dan wasan ninkaya mai kago matsayin bajinta Mr Nichael Phelps da sauransu.

Shugaban kungiyar Amurka Mr Charles Lee ya bayyana cewa,

Kowace kungiyar kasar Amurka tana kokarin horar da 'yan wasanta bisa shirye-shiryen da ta tsara. Dakin horar da su a birnin Beijing suna dakin motsa jiki na jami'ar koyar da malamai ta Beijing. A watan Yuni na shekarar da muke ciki, na taba kai ziyara a can, sharadin dakin na da kyau sosai.

Kungiyar Jamus tana kunshe da 'yan wasa da yawansu ya kai 440, kungiyar kungiya ce da ta fi girma a kasashen Turai. Tana da karfin neman samun lambobi wajen gasannin wasannin kwale-kwale da kwallon kafa tsakanin mata da tsallake-tsallake da guje-guje da lankwashe jiki da judo da kwallon tebur da sauransu. 'Yar wasan judo mai suna Annett Bohm ta bayyana cewa,

A matakin karshe, ya kamata 'yan wasanmu mu mai da hankulanmu a kan wasannin motsa jiki. A wajena, wasan motsa jiki da siyasa sun yi kama da takalmi biyu da suke rabuwa. Na amince cewa, za a yi gasannin wasannin Olimpic da kyau.

A sa'I daya kuma, kasar hadadiyyar daular larabawa da ke Gabas ta tsakiya tana sa himma ga wasannin Olimpic na Beijing tamkar yadda zafin yanayin wurin da centigrade 40 yake yi. Kasar za ta tura 'yan wasa guda 8 don halartar wasannin Olimpic na Beijing, ciki har da gimbiya Shaikha Maitha Bint Mohammad Bin rashid Al Maktoum da ke yin wasan judo da yarima Ahmed al Maktoum da ke yin wasan jefa faifai. Babban sakataren kwamitin wasannin Olimpic na kasar Mr Ibrahim Abdul Al Malek ya bayyana cewa,

Za mu sami lamba wajen wasannin harbe-harbe. A gasar wasannin Olimpic na Athens, kasarmu ta cim ma mafarkinmu na samun lambar zinariya. Za mu sa ran samun lambar zinariya a gasar wasannin Olimpic ta Beijing, wajen sauran gasanni, mu ma za mu iya samun lambobin yabo.

Ban da wadannan labaru mai faranta ran mutane, da akwai wani abun bakin ciki da ya faru, shi ne kasar Iraq ba ta sami cancancin matsayi na shiga gasannin wasannin Olimpic na Beijing. An labarta cewa, a watan Mayu na shekarar da muke ciki, bisa dalilin da karancin isasshen mutane bisa dokoki ne, gwamnatin kasar Iraq ta sanar da cewa, ta wargaje kwamitin wasannin Olimpic na kasar Iraq, kuma ta kafa kwamitin wucin gadi wanda ministan samari da motsa jiki ke kula da harkokinsa don maye gurbin tsohon kwamitin wasannin Olimpic. Sai a ranar 4 ga watan Yuni, kwamitin zataswa na wasannin Olimpic na duk duniya ya sanar da cewa, dayake gwamnatin Iraq ta tsoma baki cikin harkokin motsa jiki na kasar ta hanyar siyasa, shi ya sa kwamitin wasannin Olimpic na duniya ya zartas da kudurin sa takunkumi ga kwamitin wasannin Olimpic wajen shiga gasannin Olimpic cikin gajeren lokaci .

Sauran 'yan wasan da suka kamu da ciwace-ciwace su ma ba su da damar shiga gasar wasannin Olimpic ta Beijing, wannan abin bakin ciki ne. (Halima)