Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-09 15:20:40    
Filayen wasa na wasan Olympic a jami'o'in da ke nan Beijing(2)

cri

Dakin wasan kokawa na gasar wasan Olympic ta shekarar 2008 ta Beijing yana cikin jami'ar ilmin aikin gona ta kasar Sin da ke arewacin birnin Beijing ne. Fadinsa ya wuce murabba'in mita dubu 23. Bisa shirin da aka tsara, za a samar da kujeru dubu 8 a cikinsa, wadanda suka hada da na din din din guda dubu 6 da kuma na wucin gadi guda dubu 2.

A matsayin gini mai nuna sigar musamman da aka gina domin murnar cikon shekaru dari daya da kafuwar jami'ar ilmin aikin gona ta kasar Sin, an mai da hankali kan kimiyya da fasaha da kuma kiyaye muhalli a fannin gina dakin wasan kokawa na wasan Olympic, haka kuma, an mayar da mutane a gaban kome wajen gina shi. Da farko, tsarin nuna bayanai mai zamani da aka ajiye a cikin dakin wasan ya iya nuna wa dukkan 'yan wasan da ke babban zauren nauyin abokan karawarsu nan da nan. A fannin yin tsimin makamashi kuma, an yi amfani da zafin da aka samu daga karkashin kasa domin dumama dakin wasan, haka kuma, an yi amfani da hasken rana domin haskaka dakin wasan, saboda haka, yawan wutar lantarki da aka yi amfani da su ya ragu da kashi 30 cikin kashi dari bisa wanda a kan yi amfani da shi a sauran dakunan wasa. Bugu da kari kuma, malaman koyarwa da dalibai da suke fitowa daga kwalejojin ilmin yin amfani da ruwa da aikin injiniyan gine-gine na jami'ar sun yi nazari kan yadda za a tattara ruwan sama da ke kan rufin dakin wasan, wato yadda za a tattara ruwan sama da suka sauko a kan rufin dakin wasan domin yin amfani da shi a ban daki da kuma shayar da bishiyoyi da ciyayi.

Jami'ar ilmin aikin gona ta kasar Sin jami'a ce mafi koli a kasar Sin a fannin ilmin aikin gona. Yawan malaman koyarwa da dalibai da suke aiki da kuma karatu a cikin wannan jami'a mai tsawon shekaru dari daya ko fiye ya wuce dubu 20. Ko da yake ta shahara a duk kasar Sin saboda wasannin motsa jiki, amma duk da haka, ba ta da wani babban dakin wasa a da. Bayan da aka tabbatar da cewa, za a yi gasar wasan Olympic ta shekarar 2008 a nan Beijing, jami'ar ilmin aikin gona ta kasar Sin ta zama ta farko a cikin dukkan jami'o'in da ke Beijing da, ta gabatar da rokon gina dakin wasa na gasar wasan Olympic a cikinta. Saboda an yi nufin mayar da dakin wasan kokawa na wasan Olympic a matsayin gini mai nuna sigar musamman da aka gina domin murnar cikon shekaru dari daya da kafuwarta, shi ya sa jami'ar ilmin aikin gona ta kasar Sin ta kaddamar da gina wannan dakin wasa a ran 15 ga watan Satumba na shekarar 2005, wato a daidai ranar cikon shekaru dari daya da kafuwarta. An gina dakin wasan a wuraren rayuwa na jami'ar, a tsakanin gine-ginen gidajen dalibai guda 3 masu benaye da yawa. A ko wace rana, dubban daliban da ke fita da shiga cikin gine-ginen kan wuce ta wuraren da ake gina dakin wasan. Ta tagogin dakunansu, a ko wace rana, suna iya ganin canje-canjen da wannan dakin wasa ya samu. Irin wannan dama mai daraja, wato kusantar da kansu da gasar wasan Olympic, ba dalibai na ko wace jami'a ba ne za su iya samu.