Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-09 15:18:10    
Ziyarar shugaban kamfanin dillancin labarai na gabas ta tsakiya a Beijing ta ba shi mamaki sosai

cri

Malam Abdullah Hasan ya taba karatu a sashen watsa labarai na jami'ar Alkahira ta kasar Masar a shekaru 70 na karnin da ya gabata, kuma tun ya gama karatu har zuwa yanzu, yana aiki a kamfanin dillancin labarai na gabas ta tsakiya. A matsayinsa na wani dan jarida, ya taba shiga wasannin Olympics da gasannin cin kofin duniya da dai sauran manyan gasannin wasannin motsa jiki. Amma a wannan karo, bayan da ya kalli bikin bude gasar wasannin Olympics ta Beijing a wancan dare, ya yi farin ciki kwarai da gaske har ma ya rubuta bayani ba tare da yin barci ba, inda ya yaba wa bikin da ya zama abin koyi ga dukkan bukukuwan bude wasannin Olympics. Kuma ya bayyana cewa,

"Mun kalli wani bikin budewa mai kayatarwa a 'Shekar Tsuntsu', wanda ya nuna kwarewar Sinawa wajen tsara fasali da kuma iyawarta ba da abin koyi ga wasannin Olympics. Haka kuma ta bikin nan, na gano namijin kokarin da suka yi wajen shirya wannan biki."

A gun bikin bude gasar wasannin Olympics ta Beijing, ba kawai babban zane mai halin musamman na gabashin duniya da aka nuna ya burge malam Abdullah ba, har ma ya yi mamaki da odar wurin da aka samu yadda ya kamata, ko da kasancewar wannan gagarumin biki da kuma samun dimbin 'yan kallo. Kuma ya bayyana cewa,

"Aikin kiyaye odar bikin ya yi kyau kwarai da gaske, har ma ba a iya samun ko wane aibi ba, ba mu gamu da ko wace matsala ba yayin da muke zuwa filin wasannin motsa jiki da kuma komawa Otel. Alamar hanya da ke cikin filin wasannin motsa jiki ta nuna kofar shigowa da ta fitowa da kuma wuraren zama da ke yankuna daban daban a zahiri. Ban da wannan kuma na ga dubban matasa masu aikin sa kai a wurin, wadanda suke yin namijin kokari domin ba da jagora da kuma hidima ga 'yan kallo, sabo da haka na nuna girmamawa gare su sosai."

A cikin kwanakin kalilan da malam Abdullah ya yada zango a birnin Beijing, ban da ziyarar aiki, shi ma ya yi amfani da wannan kyakkyawar dama wajen jin dadin halin musamman na wannna birni mai dogon tarihi, shi ya sa ya ziyarci titin Niujie da aka fi samun musulmai na Beijing a ciki, da dandana abincin musulmi na titin, da kuma yin salla a masallacin da ke titin, inda ya ji ya yi kamar cikin gida. Haka kuma malam Abdullah bai manta da jin dadin halin annashuwa da ya game a ko ina a wadannan kwanaki na musamman. A matsayinsa na wani tsohun dan jarida, kuma bisa fahimtarsa ga kasar Sin, ya yi imanin cewa, tabbas ne Beijing za ta iya samun nasarar gudanar da wata gagarumar gasar wasannin Olympics. Kuma ya kara da cewa,

"Kamar yadda nake sani, kome da kome na tafiyar daidai a birnin Beijing na kasar Sin, na ga 'yan sanda da ke yin sintiri a kan tituna. Haka kuma na ga lambobin kirari a ko ina domin taya murnar shirya wasannin Olympics a Beijing da kuma maraba da zuwan masu balagoru. A cikin otel da nake ciki, ni ma na iya jin irin wannan halin Olympics. Ina fatan gwamnatin kasar Sin da jama'a Sin za su samu sanarar tafiyar da gasar wasannin Olympics."(Kande Gao)