Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-08 21:29:34    
'Yan wasa nakasassu na Kenya suna fatan za su iya samu kyawawan maki a Beijing

cri
A gun gasar wasannin Olympic ta Beijing da aka rufe a karshen watan jiya, kungiyar wasannin Olympic ta kasar Kenya ta samu lambobin yabo 14, sabo da haka, ya kai matsayi na 15 a cikin dukkan kungiyoyin da suka samu lambobin yabo, kuma ta zama kungiyar wasannin Olympic da ta samu maki mafi kyau a cikin kungiyoyin wasannin Olympic na kasashen Afirka. Bayan da aka bude gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing a ran 6 ga wata, 'yan wasa nakasassu na kasar Kenya suna fatan za su iya samun maki mai kyau kamar yadda 'yan wasa na kasar suka samu a gun gasar wasannin Olympic ta Beijing.

Kasar Kenya ta aika da 'yan wasa nakasassu 13 zuwa gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing. Daga cikinsu, 'yan wasa nakasassu 12 za su halarci gasannin guje-guje da tsalle-tsalle, wani daban kuma zai halarci gasar daga nauyi. Dukkansu sun riga sun iso Beijing domin share fagen gasar. A kwanan baya, lokacin da Douglas Sidialo, shugaban kwamitin wasannin Olympic na nakasassu na kasar Kenya yake ganawa da wakilanmu da ke kasar Kenya, ya bayyana cewa, kasar Kenya tana mai da hankali sosai kan gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing sabo da wannan gasa tana bayyana yadda ake mai da hankali kan nakasassu.

"Gasar wasannin Olympic ta nakasassu tana da muhimmanci sosai sabo da ita wata kyakkyawar dama ce inda 'yan wasa nakasassu za su iya bayyana darajarsu. Za su iya nuna wa duniya cewa, ko da yake su nakasassu ne, amma suna himmatuwa da kokarin neman cigaba kamar yadda mutane marasa nakasa suke yi. 'Yan wasa nakasassu na kasar Kenya sun taba samun kyawawan maki a gun gasannin shiyya-shiyya da na duniya. Sabo da haka, muna da imani ga makin da za su samu a gun wannan gasar wasannin Olympic ta nakasassu."

Henry Wanyoike, wani dan wasa makaho ne na kasar Kenya. A gun gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Sydney da aka yi a shekara ta 2000, ya samu wata lambar zinariya a cikin gasar gudu ta mita dubu 5. Sannan kuma ya samu lambobin zinariya 2 cikin gasannin guje-guje na mita dubu 5 da na mita dubu 10 a gun gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Athens. Sabo da haka, a gun wannan gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing, ba ma kawai yana fatan zai iya samun lambobin zinariya a cikin wadannan gasanni biyu ba, har ma yana son samun wata lambar zinariya a cikin gasar gudu ta Marathon.

"Ba zato ba tsammani ne na samu hadarin mota a watan Afrilu na shekarar da muke ciki. Daga baya na yi kokarin farfadowa da lafiya. Sannan na kara yin kokari wajen gwadawa sabo da ina son tabbatar wa sauran mutane cewa, ina da karfin halartar wannan gasa. Yanzu a shirye sosai nake. Ina fatan zan samu lambobin zinariya a gun gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing."

Mr. Henry ya taba kawo wa Beijing ziyara yau da wasu watannin da suka gabata. Lokacin da yake tabo magana kan wannan ziyara, yana farin ciki sosai.

"Wannan ziyarar da na yi cikin dan lokaci tana da kyau kwarai. Na kai ziyara a 'Shekar Tsuntsu', wato filin motsa jiki na kasar Sin da wasu sabbin tasoshin jirgin kasa da ke tafiya a karkashin kasa. Haka kuma na hau kan Babbar Ganuwa. Ina farin ciki kwarai sabo da na cimma burina."

Ban da gasannin da zai halarta, Mr. Henry zai halarci wani bikin jin kai, inda za a nemi taimakon kudin tiyata domin mutanen da suka kamu da cutar cataract a idanunsu. Mr. Henry yana fatan za a iya samun karin mutanen da su nuna goyon baya ga nakasassu da gasar wasannin Olympic ta nakasassu. "Ina son gaya wa masu sauraro na gidan rediyon kasar Sin cewa, don Allah ku nuna mu nakasassu goyon baya. Tabbas ne za mu samu nasara a gun gasar bisa goyon baya da karfin gwiwa da kuke nuna mana."