Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-08 15:24:00    
Aikin shirya gasar Olympic ta Beijing ya fi kwarewa, a cewar mataimakin shugaban kasar Kenya

cri

Kamar yadda sauran shugabannin kasashen duniya suka yi, Mr. Stephen Kalonzo Musyoka, mataimakin shugaban kasar Kenya ya halarci bikin kaddamar da gasar wasannin Olympic ta karo na 29 a nan Beijing. Bayan wannan biki, Mr. Musyoka ya kawo wa gidan rediyon kasar Sin, wato CRI ziyarar musamman. Lokacin da yake ganawa da wakiliyarmu a Beijing, Mr. Musyoka ya yaba wa bikin kaddamar da gasar wasannin Olympic ta Beijing sosai, inda ya ce, "An burge mu sosai a wancan dare, wani abin al'ajabi ne. A gun duk bikin kaddamar da gasar Olympic, ana bayyana mana karfin shirya gasar Olympic na kasar Sin. Mun sani, ba ma kawai a gun bikin kaddamar da gasar Olympic ta Beijing ne aka bayyana irin wannan karfi ba. Bayan da Beijing ya soma shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing, aikin shirya gasar da mai masaukin ya yi yana da kyau sosai. Dukkan membobin kungiyar wasannin Olympic ta kasar Kenya sun bayyana cewa, a cikin gasannin Olympic da suka halarta, aikin shirya gasar Olympic da birnin Beijing ya yi ya fi kyau."

Mr. Musyoka ya kara da cewa, a gun bikin kaddamar da gasar Olympic ta Beijing, lokacin da Mr. Yao Ming wanda ya rike tutar kasar Sin ya shugabanci kungiyar wasannin motsa jiki ta kasar Sin ya shiga filin wasannin motsa jiki na kasar Sin tare da wani yaron da ya zo daga yanki mai fama da bala'in girgizar kasa na lardin Sichuan, an burge shi sosai. "Gasar Olympic ba wani wurin gasar wasannin motsa jiki kawai ba, wannan kuma dandali ne da ke bayyana kirkin dan Adam. A gun bikin kaddamar da gasar Olympic ta Beijing, mun ga wannan kirki. A gun bikin kaddamar da gasar Olympic ta Beijing, na ga Mr. Yao Ming, wani dan wasan kwallon kwado wanda tsayinsa ya kai mita 2.26 ya shiga filin wasannin motsa jiki na kasar Sin tare da wani yaron da ya zo daga yanki mai fama da bala'in girgizar kasa. Lokacin da muke murnar bude gasar Olympic, mun kuma gai da jama'ar kasar Sin da suke fama da bala'in girgizar kasa."

An labarta cewa, kasar Kenya ta aika da wata kungiyar wasannin motsa jiki da ke kunshe da mutane fiye da dari 1 zuwa gasar Olympic ta Beijing. Wannan ne kungiyar wasannin motsa jiki mafi girma da kasar Kenya ta aika zuwa ga gasannin Olympic a tarihi. Mr. Musyoka ya ce, 'yan wasa na kasar Kenya za su yi ka'in da na'in a gun gasar.

"'Yan wasa na kasar Kenya suna gaba a kan wasannin guje-guje da tsalle-tsalle, alal misali, a gun gasannin mita dubu 1 da dubu 10 da gasar Marathon. Amma a gun wannan gasar Olympic, za mu kuma halarci sauran gasanni. Alal misali, 'yan wasanmu za su shiga gasar iyo da gasar Taekwando. Muna fatan za mu iya halartar gasar Olympic daga dukkan fannoni."

Nahiyar Afirka nahiya kadai ce da ba ta shirya gasar Olympic ba. Sabo da haka, Mr. Musyoka ya bayyana cewa, kasar Kenya tana son neman izinin shirya gasar Olympic ta shekara ta 2028.

"A cikin 'shirin neman cigaba na shekarar 2030' da gwamnatin kasar Kenya ta tsara, mun riga mun soma yin nazari kan batun neman izinin shirya wata gasar Olympic, mai yiyuwa ne za mu nemi izinin shirya gasar Olympic ta shekarar 2030. Afirka na daya daga cikin iyalan Olympic. Amma sabo da tattalin arzikinta bai samu cigaba ba, za ta sha wahala sosai domin cimma bukatar da ake nema wajen shirya wata gasar Olympic. Amma ina tsammani, za mu iya yin kokari tare, kuma za a iya cimma burin shirya wata gasar Olympic a Afirka ta hanyar yin hadin guiwa. Alal misali, abokanmu na kasar Sin za su iya taimaka mana wajen shirya gasar Olympic."

Daga karshe dai, Mr. Musyoka yana fatan gidan rediyon kasar Sin, wato CRI zai ci gaba da ba da gudummowarsa wajen sada zumunta a tsakanin jama'ar kasashen Kenya da Sin.

"Muna farin ciki muna ganin cewa, gidan CRI yana taka rawa sosai wajen sada zumunta a tsakanin jama'ar kasashen Kenya da Sin. CRI ya riga ya kafa rediyon FM a birnin Nairobi, kuma na sani, masu sauraron kasar Kenya suna son wannan rediyon FM na CRI da ke Nairobi sosai. Ina fatan kokarin da CRI ya yi zai kara samun nasara."