Yau 7 ga wata rana ce ta farko da ake gudanar da wasannin Olympic na nakasassu a nan birnin Beijing, kuma kome na gudana kamar yadda ya kamata.
Jiya 6 ga wata da dare, an yi kasaitaccen bikin fara wasannin Olympic na nakasassu a babban filin wasannin kasar Sin da ke nan birnin Beijing. 'Yan kallo sun nuna babban yabo sosai ga bikin. Jose Palleres, dan kallo da ya zo daga kasar Spain, ya ce, yana da imanin cewa, wasannin Olympic na nakasassu za su kasance masu kayatarwa tamkar wasannin Olympic da aka rufe su kwanan baya ba da jimawa ba.Ya ce,"Bikin ya ba mu mamaki sosai, kuma ya shere mu, ina sonsa sosai. Wasannin Olympic na nakasassu ya fi karfafa gwiwar jama'a, sabo da dole ne 'yan wasa nakasassu su yi namijin kokari. Wasannin Olympic na Beijing sun ciyar da wasannin Olympic zuwa wani babban matsayi, sabo da haka, ina da imanin cewa, wasannin Olympic na nakasassu da za a fara yi za su kasance masu kayatarwa sosai, kuma birnin Beijing ya yi gaggarumin aiki domin gudanar da wasannin."
Daidai kamar yadda Jose ya ce, tun tuni Beijing ya fara share fagen wasannin Olympic na nakasassu. A cikin kwanaki sama da 10 da suka wuce tun bayan da aka rufe wasannin Olympic har zuwa lokacin da aka fara wasannin Olympic na nakasassu, Beijing ta yi kokari wajen cimma burinta na "gudanar da wasannin Olympic na nakasassu masu kayatarwa kamar yadda aka gudanar da wasanin Olympic".
A cikin kwanaki 11 masu zuwa, 'yan wasa sama da dubu 4 da suka zo daga kasashe daban daban za su shiga gasanni a manyan fannoni 20. Yau 7 ga wata, wato rana ta farko da aka fara gasar wasannin Olympic na nakasassu, an fara gasar wasannin harbe-harbe da iyo da hawan keke da Judo da dai sauransu. Daga cikinsu kuma, an kaddamar da lambar zinari ta farko ta wasannin nakasassu a wannan karo a gun gasar harbe-harben rifle na mita 10 na mata. Veronika Vadovicova, wadda ta sami wannan lambar yabo, ta ce, ta gamsu da na'urorin gidan wasan harbe-harbe da kuma hidimar da ake samarwa, ta ce,"Ina ganin kome na gudana yadda ya kamata, kuma masu aikin sa kai suna da zumunci, na gamsu sosai."
Bayan da aka fara wasannin Olympic na nakasassu, manema labarai na kasashe daban daban su fara ayyukansu. Ana iya ganinsu ko ina a cikin filayen wasa da kuma cibiyar manema labarai ta wasannin Olympic na nakasassu. Tabbatar da ayyukansu da su gudana yadda ya kamata shi ma ya zama wani muhimmin aiki wajen gudanar da wasannin Olympic na nakasassu.
A ofishin 'yan jarida da ke cibiyar manema labarai na wasannin Olympic na nakasassu, manema labarai na iya tuntubar ma'aikatan ofishin su nemi taimako, idan suna da matsala. Madam Hu Liu, manajar ofishin 'yan jarida da ke cibiyar, ta ce, za su yi iyakacin kokari wajen tabbatar da ayyukan manema labarai su gudana yadda ya kamata. ta ce,"lokacin da manema labarai suka zo wurinmu neman bayani ko ba da tambaya, mu kan samar musu hidima mafi inganci, mu taimaka musu daidaita matsalolin cikin gajeren lokci, ta yadda za su iya gudanar da ayyukansu yadda ya kamata."
A yayin da yake jawabi a gun bikin fara wasannin Olympic na nakasassu a jiya 6 ga wata da dare, shugaban kwamitin wasannin Olympic na nakasassu na duniya, Mr.Philip Craven ya ce, wasannin Olympic na nakasassu na Beijing zai zama wata ishara a tarihin wasannin Olympic na nakasassu. Ya ce, wasannin Olympic na Beijing na da matukar kayatarwa, kuma tabbas ne za a cimma nasarar gudanar da wasannin Olympic na nakasassu a Beijing. Bari mu sa rai ga wasannin Olympic na nakasassu masu kayatarwa kamar yadda aka gudanar da wasannin Olympic na Beijing.(Lubabatu)
|