Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-06 18:07:49    
Shugaban kasar Sin ya shirya liyafa domin kaggan bakin da suke halartar gasar Olympic ta nakasassu ta Beijing

cri

A ran 6 ga wata da tsakar rana, shugaban kasar Sin Hu Jintao da matarsa sun shirya wata gagarumar liyafa a babban dakin taron jama'a na Beijing domin maraba da manyan bakin da suka zo kasar Sin domin halartar gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing. A cikin jawabin da ya yi a gun liyafar, Mr. Hu ya bayyana cewa, gwamnati da jama'a na kasar Sin suna da imanin shirya wata ingantacciyar gasar wasannin Olympic ta nakasassu da ke nuna halayen musamman. Yana kuma fatan wannan gasar wasannin Olympic ta nakasassu za ta zama wani dandamalin kara fahimtar juna da sada zumunci a tsakanin nakasassu na kasashe da yankuna daban daban. Yanzu ga wani cikakken bayanin da wakilanmu suka aiko mana game da wannan liyafa.

"Mr. Craven, shugaban kwamitin wasannin Olympic na nakasassu na kasa da kasa da matarsa"

A ran 6 ga wata da rana, bi da bi ne manyan baki kusan 80 na kasashen duniya, ciki har da Philip Craven, shugaban kwamitin wasannin Olympic na nakasassu na kasa da kasa da Antonio Samaranch, shugaba mai martaba na kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa da yarima na kasar Luxemburg da firayin minisatan kasar Koriya ta kudu, suka iso babban dakin taron jama'a na Beijing. Hu Jintao da matarsa wadanda suke jiransu sun yi musafaha da su. Kamar yadda aka shirya liyafa domin manyan bakin da suka halarci gasar wasannin Olympic ta Beijing, an kawatar da dakin liyafa sosai. Amma ya kasance da wani abin daban, wato a kan hawa guda ne an yi bikin maraba da zuwan manyan baki da liyafar domin manyan baki nakasassu. A lokacin da aka soma liyafar, dai farko dai, Hu Jintao ya nuna maraba da zuwan manyan baki.

"Da farko a madadin gwamnati da jama'ar kasar Sin ne ina maraba da zuwan dukkan manyan baki a gun gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing da hannu biyu biyu. Kuma cikin sahihanci ne ina godiya ga dukkan abokai wadanda suka bayar da gudummowa ga gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing."

Sannan kuma, Hu Jintao ya bayyana cewa, kasar Sin tana da nakasassu miliyan 80. Sabo da haka, gwamnati da jama'ar kasar Sin suna mai da hankali kan harkokin nakasassu a kullum, kuma ta riga ta dauki jerin matakai domin ciyar da harkokin nakasassu gaba daga dukkan fannoni. A waje daya kuma, kasar Sin za ta yi amfani da wannan damar shirya gasar wasanin Olympic ta nakasassu ta Beijing wajen kiyaye iko da moriyar nakasassu. Mr. Hu ya ce, "Za mu yi amfani da wannan damar shirya gasar Olympic ta nakasassu ta Beijing domin kara yada tunanin mutumtaka na jin kai da yin kokari wajen kiyaye halaltaccen iko da moriyar nakasassu, da kuma tabbatar da ganin nakasassu sun shiga zaman al'umma da more sakamakon tattalin arziki da zaman al'umma cikin halin daidai wa daida."

'Yan wasa fiye da dubu 4 da suka zo daga kasashe da yankuna 148 za su shiga gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing. Sabo da haka, an riga an samar da ayyuka da na'urori marasa shinge a dukkan dakuna da filaye na motsa jiki da wuraren yawon shakatawa da kayayyakin abeben hawa da nakasassu za su je ko za su yi amfani da su. Mr. Hu ya bayyana cewa, kasar Sin ta riga ta yi namijin kokarinta wajen shirya gasar Olympic ta nakasassu ta Beijing. Mr. Hu ya ce, "Bayan da aka samu izinin shirya gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing a shekara ta 2001, gwamnati da jama'a na kasar Sin sun yi kokarin aiwatar da alkawarin da suka dauka a karkashin taimakawar kwamitin wasannin Olympic na nakasassu na kasa da kasa da sauran al'ummomin duniya. Ta shirya wannan gasa ne bisa hasashe uku, wato 'wucewa da haduwa da morewa' da kuma shirya gasannin Olympic biyu masu kayatarwa tare. Ina cike da imani cewa, a karkashin goyon bayan da kwamitin wasannin Olympic na nakasassu na kasa da kasa da sauran al'ummomin duniya suke nuna mana, tabbas ne gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing za ta zama wata gasar Olympic ta nakasassu mai inganci da ke nuna halayen musamman." (Sanusi Chen)