Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-05 21:45:50    
Lamura da dama masu faranta rai da suka wakana a gasar wasannin Olympics ta Munich

cri

A gun zama na 64 na kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa da aka gudunar a shekarar 1966, birnin Munich na Tarayyar Jamus wadda a karo na farko ne ta gabatar da rokon shirya gasar wasannin Olympics ya samu iznin shirya gasar wasannin Olympics ta 20 ta yanayin zafi a shekarar 1972 bayan da aka jefe kuri'a har zagaye biyu. Kasar Jamus ta sake gudanar da gasar wasannin Olympics bayan babban yakin duniya na biyu, hakan ya girgiza da kuma faranta ran muanen duk duniya. " Yanzu bari in shelanta cewa a bude gasar wasannin Olympics ta 20 ta shekarar 1972 a Munich!"

Nan take halin annashuwa ya game duk filin wasannin motsa jiki na Olympics na Munich yayin da shugaban Tarayyar Jamus Mr. Gustav Heinemann na lokacin ya yi shelar din. Hakan ya shaida cewa, aka sake dawo da wasannin Olympics cikin yankin Turai shekaru 12 bayan da aka rufe gasar wasannin Olympics ta Rome; haka kuma a karo na farko ne aka gudanar da gasar wasannin Olympics a kasar Jamus bayan babban yakin duniya na biyu. A lokacin, gwamnatin birnin Munich ya kaddadmar da alkiblar gudanar da gasar a kan cewa " Kusantowa da juna" da " A hada al'adun birane da rayuwar zaman yau da kullum"; Kazalika, ta mayar da " gudanar da gasar wasannin Olympics cikin halin fara'a a matsayin kirarin gasar wasannin" da kuma "bikin al'ummomi". Jami'in sashen kula da yin cudanya na kamfanin lambun shan iska na Munich Mr. Arno Hartung ya furta cewa: " A lokacin, kasashen Jamus na gabas da na yamma a rabuwa suke. Amma bayan mulkin Nazi na Hitlerr da daula ta uku da kuma babban yakin duniya na biyu, kasar Jamus na kishin gwada fuskarta ta zamani da 'yanci da demokuradiyya da kuma ta bude kofa a gaban dukkan kasashen duniya. Sakamakon haka, ta cimma burinta ta yin la'akari da siyasa yayin da take gudanar da gasar wasannin Olympics".

Jama'a masu saurare, girman sikelin gasar wasannin Olympics ta Munich ya kirkiro matsayin bajinta, wato ke nan gasar din ta sami halartar 'yan wasa da yawansu ya kai 7,173 daga kasashe da shiyyoyi 121, wadanda suka shiga manyan ayyukan wasa 23 da kuma kananan ayyukan wasa 195. Kokawa da aka yi tsakanin 'yan wasa na Tarayyar Jamus da na Jamus ta Demokuradiyya a gun gasanni ta fi janyo hankulan masu kallo.

A cikin sowwar murna da masu kallo 80,000 suka yi a gun filin wasannin motsa jiki na Olympics na Munich, kungiyar Jamus ta Yamma ta lashe kungiyar Jamus ta Gabas wato ta kwashi lambar zinariya a gun gasar karshe ta gudun yada kanin wani na tsawon mita 400 na mata hudu-hudu. Shugaban hukumar kula da harkokin wasannin motsa jiki ta birnin Munich Mr.Rugolf Behacker ya yi farin ciki da waiwayen yadda 'yan wasa na Jamus ta Yamma suka nuna kwarewa a gun gasanni, yana mai cewa :' Ai lallai ban manta da gasar karshe ta wasan boli na maza da aka yi tsakanin 'yan wasa na kasashen Japan da Jamus ta demokuradiyya. Bayan shekaru 25, gwamnatin birnin Munich ta gayyaci 'yan wasa na wadannan kungiyoyi guda biyu na wancan lokaci don su sake haduwa gu daya. Ban da wannan kuma, an taba samun ' Ranar Lahadi ta zinariya', wato ke nan a wannan rana ne 'yan wasa na Jamus ta Yamma suka kwashe lambobin zinariya guda uku a cikin dukkan gasannin karshe iri biyar'.

Jama'a masu saurare, wani abu daban mai ban sha'awa na gasar wasannin Olympics ta Munich shi ne an haifar da abun dake kawo sa'a na farko a tarihin wasannin Olympics na yanayin zafi. An kuma lakaba masa sunan Waldi mai siffar karamin kare kuma mai launi iri daban-daban dake alamanta babbar kasa da sararin sama na Jamus.

Ban da wadannan kuma, an samu lambun shan iska na Olympics na Munich wanda shi ne ya kasance wani shahararren kayan gado na gine-gine a duniya bayan gasar wasannin na Olympics da aka gudanar. ( Sani Wang)