Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-05 18:57:50    
Beijing a shirye yake wajen gudanar da gasar wasannin Olympic ta nakasassu

cri

Ran 6 ga wata, za a bude gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing. A ran 5 ga wata, wato ranar kafin bude gasar, a gun taron manema labaru da aka yi a babbar cibiyar yada labaru ta gasar wasannin Olympic ta nakasassu, jami'an kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing sun bayyana cewa, yanzu Beijing a shirye yake baki daya wajen gudanar da gasar wasannin Olympic ta nakasassu.

A matsayinta na kungiyar 'yan wasa ta farko da ta zo daga kasashen waje, ta daga tutar kasa a kauyen wasannin Olympic na nakasassu na Beijing, mambobin kungiyar 'yan wasa ta kasar Slovenia da suka zo Beijing yau da kwanaki da dama da suka wuce sun dauki jagoranci wajen yin amfani da na'urorin da ke kauyen. Dan wasan jefa faifan karfe Joze Flere na Slovenia ya nuna gamsuwa sosai, ya ce,'A ko wane lokaci ana ba da hidima mai kyau a ko ina na kauyen wasannin Olympic na nakasassu. A bayyane ne ake ba da hidima mai taurari 5. In ba ka zo wannan kauyen ba, ba za ka iya kiyasta kyaunsa ba.'

An yi kwaskwarima kan kauyen wasannin Olympic daga dimbin kananan fannoni domin nakasassu, ta haka an samu kauyen wasannin Olympic na nakasassu da muka gani a yau.

Ban da wannan kuma, dukkan filaye da dakunan wasa 19 da na aikin horo 7 da ke da nasaba da gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing sun biya bukatu, an kuma riga an gama jarraba na'urori marasa shinge da ke cikinsu.

Domin raya birni maras shinge, Beijing ya bayar da kokari sosai. Yau da shekaru da dama da suka wuce, Beijing ya fara shimfida hanyoyin musamman domin makaho a duk fadin birnin, ya kuma kafa tasoshin jiragen kasa da ke karkashin kasa da gadoji da hanyoyin da ke karkashin kasa da nakasassu masu amfani da keken hannu da kuma makaho suka iya amfani da su, ban da wannan kuma, ya sa kaimi kan raya muhimman ayyukan ba da hidima ga al'umma domin biyan bukatun nakasassu.

Saboda kusantowar gasar wasannin Olympic ta nakasassu, ma'aikata da masu aikin sa kai da za su ba da hidima a lokacin gasar wasannin Olympic ta nakasassu a shirye suke. A gun taron manema labaru da aka yi a ran 5 ga wata, Wang Wei, mataimakin shugaban zartaswa na kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing ya bayyana cewa,'Yanzu ma'aikatan kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing a shirye suke. Dukkan ma'aikata dubu 178 sun yi rajista. Masu aikin sa kai kuwa a shirye suke. Ban da wannan kuma, 'yan jaridu fiye da 6300 sun gama yin rajista. A galibi dai, dukkan mutane a shirye suke.'

1 2