Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-05 16:25:03    
Kasashen Afirka suna fatan za a kara zuba jari a fannin tsabtaccen makamashi da ba ya gurbata muhalli

cri

An rufe dandalin tattaunawa kan gawayi na Afirka na karo na farko, wanda aka shafi kwanaki uku ana yinsa a birnin Dakar, babban birnin kasar Senegal. Babban makasudin wannan dandalin tattaunawa shi ne, domin sa kaimi ga kasashe masu sukuni da su kara zuba jari kan ayyukan tsarin samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli a kasashen Afirka, da kuma rage fitar da hayaki na carbon-dioxid da ke dumamar yanayi, da kuma rage sauyawar yanayin duniya, a sa'i daya kuma, sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki cikin dogon lokaci a kasashe masu tasowa.

A hakika dai, tsarin samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba, wata hanya ce da kasashe masu sukuni suke bi wajen cim ma burin rage fitar da iska da ke dumamar yanayi. Bisa abubuwan da aka tanada a cikin 'Takardar bayani ta Kyoto', an ce, daga shekarar 2008 zuwa ta 2012, ya kamata kasashe masu sukuni su rage yawan iskar da ke dumama yanayi da kashi 5.2 daga cikin dari bisa na shekarar 1990. Amma kudin da kasashe masu sukuni suka kashe wajen rage irin wannan iska ya fi na kasashe masu tasowa yawa, kasashe masu sukuni ba su iya biya bukatarsu da kansu ba. Sabo da haka ne, kasashe masu sukuni da yawa suka bayyana cewa, suna fuskatar wasu matsaloli wajen cim ma wannan buri. Tsarin samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba ya yarda da kasashe masu sukuni su bi hanyar ba da kudi ko fasahohi domin taimakawa kasashe masu tasowa wajen raya sha'anonin tsabtaccen makamashi da dai sauran ayyukan da ke iya rage dumamar yanayi, bayan da aka amince da yawan iskar da aka rage, za a iya mayar da su a matsayin sakamakon da kasashe masu sukuni suka samu, domin taimaka musu wajen cim ma burin rage iskar da ke dumama yanayi.

Amma a yayin da kasashe masu tasowa da yawa suke samun moriya daga tsarin samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba, an manta da nahiyar Afirka. Bisa rahoton da bankin duniya ya bayar a lokacin da ake gudanar da dandalin, an ce, a halin yanzu dai, yawan ayyukan kara samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba a duk duniya ya kai 3902, amma 53 daga cikinsu kawai, ana gudanar da su ne a Afirka. Rahoton yana ganin cewa, dalilin da ya sa hakan shi ne, domin masu zuba jari ba su san nahiyar Afirka sosai ba. Sabo da haka ne, sakataren zartarwa na yarjejeniyar sauyawar yanayi ta MDD Mr. Yvo De Boer ya yi fatan wannan dandalin tattaunawa zai iya jawo hankulan masu zuba jari ga Afirka. Haka kuma ya sa kaimi ga kasashen Afirka da su yi amfani da wannan kyakkyawar dama, su kara yin mu'amala da masu zuba jari da kungiyoyi da hukumomin duniya, domin masu zuba jari su karfafa imani ga kasashensu.(Danladi)